Sulaiman Ibrahim" />

#ENDSARS: Mutum Daya Ya Mutu Yayin Da Aka Kona Ofishin ‘Yan Sanda A Legas

Ayau Talata ne wasu ‘yan daba a rigar masu zanga-zangar #ENDSARS suka kona ofishin ‘yan sanda na Shiyyar Orile Iganmu da ke jihar Legas.

Wani wakilin kamfanin dillacin labarai na Nijeriya (NAN), wanda yake wurin, ya ruwaito cewa wasu ‘yan iska sun far wa ofishin ‘yan sandan, inda suka banka wa ofishin wuta ta hanyar amfani da man fetur.

Wannan yasa Wasu ‘yan sanda a ofishin suka fara harbi kan mai-uwa-dawabi a kan taron masu zanga-zangar.

Anga gawa da raunuka ajikinta yayin da abin ya faru.

Gaba daya tashar motar Orile Iganmu an jefata cikin hautsini.

Hanyar kasa-da-kasa ta babban titin Lagos / Badagry ta zama a cunkushe yayin da masu ababen hawa ke hanzarin juyawa don kare lafiyarsu a yayin musayar wutar. (NAN)

Exit mobile version