Rundunar ‘yan sandan Nijeriya ta shigar da kara gaban kotun tarayya da ke Abuja ta na bukatar umarnin kotun na dakatar da kwamitocin binciken da aka kafa don bincikenta.
Kwamitocin binciken wanda gwamnoni suka kafa domin bankadowa da gano zarge-zargen cin zarafin al’umma da ake zargin jami’an rushashshiyar tawagar SARS, da sauran ‘yan sanda da aikatawa ga jama’a.
Kwamitocin wanda majalisar kolin Nijeriya (NEC) ta bada umarnin kaddamarwa a yayin zaman da mataimakin shugaban kasa Farfesa Yemi Osinbajo ya jagoranta kan matsalolin da aka fuskanta na EndSARS a watan Oktoba.
“A gaggauta kaddamar da kwamitocin bincike a jihohin kasar nan tare da amsa da tattarowa, binciko korafe-korafen cin zarafin jama’a da kisan rashin kan gado da ake zargin aikatawa domin tabbatar da adalci ga wadanda lamarin ya shafa daga rundunar SARS,” matsayar NEC a ganawarta na watan Oktoba.
Ya kara da cewa, gwamnatocin jihohi ba su da iko ko damar kafa kwamitocin binciken ayyukan ‘yan sandan Nijeriya da jami’anta kamar yadda doka ya tanadar.
Don hakan, ‘yan sandan sun roki kotun ta umarci Antoni-Antoni da suke fadin jihohin kasar nan 36 da kwamitocinsu da su daina gudanar da wani zama don binciken ayyukan ‘yan sanda balle tuhumarsu.
A cewar ‘yan sanda, matakin gwamnatocin jihihohin ya take doka sashi na 241(1)(2)(a) da Item 45, Part 1, First Schedule na dokokin kasa gami da doka sashi na 21 na dokar Tribunals of Inkuiry.
Lauyan ya ce dokokin sun baiwa gwamnatin tarayya ne kawai ikon daidaitawa da shawo kan lamuran ‘yan sanda, amma ba jihohi ba.
Kes din wanda aka ware ranar 3 ga Disamba domin sauraronsa amma an dage zuwa ranar 18 ga Disamba sakamakon cewa kotun tarayyar ba ta zauna ba a jiyan.
Wakilinmu ya nakalto cewa kwamitocin da aka kafa don binciken cin zarafin da ‘yan sanda suka yi wa jama’a a jihohi na samun jagoranta ne daga tsoffin Alkalai a fadin kasar nan wanda aka sanya mambobin kungiyoyin fararen hula, masu kare hakkin jama’a, matasa, Lauyoyi da sauransu a matsayin mambobi.
A jihar Legas kawai, kwamitin binciken ya amshi korafe-korafe sama da 110 wanda ake tsammanin samun wasu karin koke da dama, kana ana sa ran sauraron keken jama’an daga masu korafi tare da gabatar da shaidunsu.