Abba Ibrahim Wada" />

Eto’o Ya Roki Kamaru Akan Sakin Iya Muhammad

Tsohon kaftin din kungiyar kwalon kafar kasar Kamaru ta Indomitable Lions, Samuel Eto’o Fils, ya nuna damuwa kan ci gaba da tsare tsohon shugaban hukumar kwalon kafar kasar Iya Mohammed, inda ya roki shugaban kasa Paul Biya da yayi wa Allah ya sake shi.

Cikin wata hira da aka watsa kai tsaye a wasu gidajen radio 4 na kasar Kamaru a ranar Alhamis ne, Samuel Eto’o wanda bai nuna nadamar kokarin da ya yi a lokacin da yake Kaftin din tawagar, tsakanin shekarun 2011 zuwa 2013, wajen ganin Iya Mohammed ya bar jagorancin kungiyar kwalon kafar kasar ba.

A watan Yuni shekarar 2013, ne mahukuntan Kamaru suka garkame Iya Mohammed a kurkun kwandengi, bayan dawowarsa daga rakiyar ‘yan wasan kasar daga kasar Togo, kuma tun daga wancan lokaci aka ci gaba da tsare shi, bisa zargin albazaranci da kudin Kamafanin audugar kasar Sodecoton da can ma yake jagoranta.

Kuma tun bayan tsare shi, makusantar Iya, ke zargin Samuel Eto’o da shirya makarkashiya domin cire shi daga shugabancin kungiyar, ganin fada-aji da Eto ke da shi a gwamnatin kasar, da kuma rashin dasawarsu da iya Muhammad.

Yanzu dai ta tabbata ta kare, Samuel Eto’o ya tabbatar da wannan zargi kai tsaye a kafafen radion, dangene da bita da kullin da ya yiwa dan asalin yankin arewacin kasar, kuma tsohon shugaban kungiyar kwallon kafar kasar, kuma shugaban kamfanin audugar kasar, kana mamallakin kungiyar kwallon kafar jihar sa Garoua, wato Coton Sports da tayi suna a kasashen Afrika dama duniya, da yanzu haka ya kwashe shekaru 6 a kurku.

Sai dai wata majiya ta bayyana cewa shugaban kasar bashi da niyyar sakin Iya Muhammad amma kuma tunda dan wasa Samuel Eto’o yayi Magana watakila ya kalli lamarin kuma ya bayar da umarnin sakinsa.

Exit mobile version