EU Na Shirin Kakaba Harajin Wucin Gadi Kan Ababen Hawa Masu Amfani Da Lantarki Kirar Kasar Sin
  • English
  • Business News
Wednesday, October 8, 2025
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

EU Na Shirin Kakaba Harajin Wucin Gadi Kan Ababen Hawa Masu Amfani Da Lantarki Kirar Kasar Sin

byCGTN Hausa
1 year ago
EU

Kakakin ma’aikatar cinikayya ta kasar Sin, ya ce kungiyar tarayyar Turai EU, na shirin kakaba harajin wucin gadi, kan ababen hawa masu amfani da lantarki kirar kasar Sin, wadanda ake shigarwa kasashe mambobin kungiyar ta EU, a wani yunkurin na cike gibin kudaden rangwame da EUn ke zargin an samarwa kamfanonin da suke kera motocin a Sin.

Kakakin, wanda ya yi tsokacin a Larabar nan, ya ce EU ba ta bi ka’ida wajen daukar wannan mataki ba, ta kuma yi watsi da gaskiya, da ka’idojin kungiyar cinikayya ta duniya WTO, kana ta yi watsi da kakkarfar adawar da Sin ta sha yi kan matakin. Kaza lika ta kawar da kai daga kiraye-kiraye, da jan hankali daga gwamnatocin kasashe mambobin EUn masu yawa, da kamfanonin kasashen kungiyar.

  • Ministan Harkokin Wajen Kasar Sin Ya Halarci Taron Ministocin BRICS Da Kuma Gana Da Takwarorinsa Na Habasha Da Afirka Ta Kudu
  • Xi Ya Ba Da Amsa Ga Wasikar Farfesan Jami’ar Tsinghua

Ya ce Sin ta yi matukar damuwa, tare da nuna rashin amincewa da matakin. Tana kuma kira ga EU, da ta gaggauta gyara wannan kuskure, kuma Sin din za ta zura ido sosai kan matakan EUn na gaba, tare da daukar dukkanin matakan da suka wajaba, domin kare halastattun hakkoki, da moriyar kamfanonin ta.

Har ila yau, a dai wannan rana, kungiyar kamfanonin kirar motoci ta kasar Sin, ta bayyana fatan cewa, EU ba za ta siyasantar da batutuwan da suka jibanci tattalin arziki da cinikayya ba, kana ba za ta keta hurumin tsare tsaren cinikayya ba. (Mai fassara: Saminu Alhassan)

ShareTweetSendShare

MASU ALAKA

Yawan Zirga-Zirgar Jiragen Kasa Tsakanin Sin Da Turai Kan Layin Dogo Na Tsakiya Ya Zarce 3,000 A Bana
Daga Birnin Sin

Yawan Zirga-Zirgar Jiragen Kasa Tsakanin Sin Da Turai Kan Layin Dogo Na Tsakiya Ya Zarce 3,000 A Bana

October 8, 2025
Adadin Kudaden Da Gidajen Sinima Na Sin Suka Tara Yayin Hutun Bikin Ranar Kasa Ya Haura Yuan Biliyan 1.7
Daga Birnin Sin

Adadin Kudaden Da Gidajen Sinima Na Sin Suka Tara Yayin Hutun Bikin Ranar Kasa Ya Haura Yuan Biliyan 1.7

October 8, 2025
Sin: Ana Sa Ran Jigilar Fasinjoji Fiye Da Miliyan 21 A Yau Ta Jiragen Kasa
Daga Birnin Sin

Sin: Ana Sa Ran Jigilar Fasinjoji Fiye Da Miliyan 21 A Yau Ta Jiragen Kasa

October 8, 2025
Next Post
Xi Ya Gabatar Da Jawabin Bude Taron Cika Shekaru 60 Da Kafuwar UNCTAD Ta Kafar Bidiyo

Xi Ya Gabatar Da Jawabin Bude Taron Cika Shekaru 60 Da Kafuwar UNCTAD Ta Kafar Bidiyo

LABARAI MASU NASABA

Yawan Zirga-Zirgar Jiragen Kasa Tsakanin Sin Da Turai Kan Layin Dogo Na Tsakiya Ya Zarce 3,000 A Bana

Yawan Zirga-Zirgar Jiragen Kasa Tsakanin Sin Da Turai Kan Layin Dogo Na Tsakiya Ya Zarce 3,000 A Bana

October 8, 2025
Majalisa Ta Nemi Jami’an Tsaro Su Ceto Daliban Jami’ar Gusau 30 Da Aka Sace

Kafa ‘Yansandan Jihohi Na Da Matuƙar Muhimmanci Wajen Magance Matsalar Rashin Tsaro

October 8, 2025
Adadin Kudaden Da Gidajen Sinima Na Sin Suka Tara Yayin Hutun Bikin Ranar Kasa Ya Haura Yuan Biliyan 1.7

Adadin Kudaden Da Gidajen Sinima Na Sin Suka Tara Yayin Hutun Bikin Ranar Kasa Ya Haura Yuan Biliyan 1.7

October 8, 2025
Tinubu

Tinubu Na Son A Saka Hannun Jari Da Kuɗaɗen Fansho A Ɓangaren Mai Da Iskar Gas

October 8, 2025
Gwamnatin Nasarawa Za Ta Hukunta Duk Masu Amfani Da Sinadiran Kamun Kifi Acikin Ruwa

Gwamnatin Nasarawa Za Ta Hukunta Duk Masu Amfani Da Sinadiran Kamun Kifi Acikin Ruwa

October 8, 2025
Sin: Ana Sa Ran Jigilar Fasinjoji Fiye Da Miliyan 21 A Yau Ta Jiragen Kasa

Sin: Ana Sa Ran Jigilar Fasinjoji Fiye Da Miliyan 21 A Yau Ta Jiragen Kasa

October 8, 2025
Kwastam Ta Kama Lita 35,000 Na Man Fetur, Tabar Wiwi Da Sauran Kayayyaki A Kebbi

Kwastam Ta Kama Lita 35,000 Na Man Fetur, Tabar Wiwi Da Sauran Kayayyaki A Kebbi

October 8, 2025
Sin Ta Yi Kira Ga Mambobin WTO Da Su Tinkari Yanayin Tangal-Tangal Tare

Sin Ta Yi Kira Ga Mambobin WTO Da Su Tinkari Yanayin Tangal-Tangal Tare

October 8, 2025
ABU Na Kashe Sama Da Naira Biliyan 4 Duk Shekara A Wutar Lantarki

ABU Na Kashe Sama Da Naira Biliyan 4 Duk Shekara A Wutar Lantarki

October 8, 2025
Gwamnati Ta Roƙi ASUU Ta Soke Shiga Tsunduma Yajin Aiki, Ta Yi Alƙawarin Biyan Buƙatunsu

Gwamnati Ta Roƙi ASUU Ta Soke Shiga Tsunduma Yajin Aiki, Ta Yi Alƙawarin Biyan Buƙatunsu

October 8, 2025

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

Exit mobile version