Bello Hamza" />

EU Ta Gargadi Kasashe Kan Yi Wa Benezuela Katsalandan Din Soji

Kungiyar Tarayyar Turai EU ta gargadi kasashen duniya kan illar yi wa Benezuela katsalandan din Soji a harkokinta, dai dai lokacin da rikici ya dabaibaye kasar da nufin samar da maslahar dimokaradiyya wajen shawon kan rikicin.
A cewar Maja Kocijancic kakakin shugabar Ofishin kula da manufofin diflomasiyyar Tarayyar Turai a kasashen duniya Federica Mogherini, a wata ganawarta da manema labarai, ta ce babu bukatar sai an sanya karfin soji kafin warware rikicin kasar ta Benezuela, matukar zai iya warwaruwa ta hanyar dimokaradiyya.
Tun a makon da ya gabata ne dai yayin taron shugabannin kasashen Turai da ya gudana a Brussels, suka cimma matsayar kin mara baya wajen amfani da karfin soji a kasar ta Benezuela.
Shima ministan harkokin wajen Spain, Josep Borell, ya shaida wa manema labarai cewa shugabannin Turai sun yi kashedi ga dukannin kasashen da ke tunanin yin katsalandan a Benezuela ta wajen aikewa da dakarunsu cewa ba za su goyi bayan hakan ba, kuma za su soki abin ba kakautawa.
Jagoran ‘yan adawa a kasar ta Benezuela, wanda ya bayyana kansa a matsayin shugaban kasa, Juan Guaido yana birnin Bogota na Colombia inda yake tattaunawa da abokan huldarsa na nahiyar don lalubo hanyar da za a bi wajen tilasta wa shugaban Benezuela Nicolas Maduro ya sauka daga mukaminsa.
Taron na Bogota na zuwa ne kwanaki biyu bayan mutane biyu sun mutu, daruruwa suka jikkata yayin wata arangama tsakanin magoya bayan Guaido da jami’en tsaron Bnezuela yayin wani kokarin shigowa da kayayyakin agaji daga Colombia da Brazil da ya ci tura.

Exit mobile version