EU Ta Soki Rashin Daidaito A Zaben Kasar Mozambik

Masu sa ido na kungiyar tarayyar Turai wadanda suka lura da zaben kasar Mozambik sun ce an nuna fifiko wajen bai wa jam’iyyu damar amfani da kafofin gwamnati a zaben shugaban kasar da ya gudana

Tawagar sa ido ta kungiyar tarayyar Turai ta soki lamirin zaben Mozambik ta na mai cewa ba a nuna daidaito da adalci wajen amfani da kayayyakin gwamnati ba inda jam’iyya mai mulki ta kankane komai sannan an sami tashin hankali a wurare da dama.

Kawo yanzu dai ba a sami sakamakon zaben shugaban kasar da aka gudanar a ranar Talata ba. Sai dai ana gani sakamakon zai kasance zakaran gwajin dafi na zaman lafiyar da ke tangal-tangal tsakanin jam’iyya mai mulki ta Frelimo da babbar abokiyar adawarta ta Renamo da suka gwabza yaki.

A waje guda dai tawagar sa ido ta Afirka wadda tsohon shugaban Nijeriya Goodluck Jonathan yake jagoranta da kuma kungiyar raya kasashen kudancin Afirka SADC sun yaba wa zaben da cewa ya gudana lami lafiya cikin kwanciyar hankali.

Exit mobile version