Euro 2020: Ingila Ta Fara Binciken Rashin Da’ar Magoya Bayan Kasar

Ingila

Hukumar kula da kwallon kafar Ingila ta ce, ta dukufa wajen tabbatar da cewa, ba a sake maimaita abin kunyar da aka aikata a yayin wasan karshe na gasar cin kofin kasashen turai ta Euro 2020 ba.

Hukumar ta FA ta ce, za a gudanar da bincike mai zaman kansa game da yadda aka keta matakan tsaro a yayin wasan wanda hakan yasa wasu mutanen da dama suka shiga filin wasan ba tare da sun biya kudi ba sannan aka bar wadanda suka biya kudi a waje basu samu damar shiga ba saboda turmutsutsu.

Magoya bayan tawagar ‘yan wasan Ingila sun yi arangama da jami’an tsaro a yayin yunkurinsu na kutsawa cikin filin wasan na Wembley a ranar 11 ga watan nan na Yuli duk da cewa ba su sayi tikiti ba.

Tuni Hukumar kwallon kafar Turai ta UEFA ta gabatar da tuhume-tuhume guda hudu ga Hukumar kwallo kafar Ingila kan wannan muguwar dabi’ar da magoya bayan kasar suka nuna a lokacin gasar.

Daga cikin abin da magoya bayan na Ingila suka aikata har da jefe-jefe da karikitai da kunna tartsatsin wuta da kuma yin ihu a lokacin da ‘yan wasan Italiya ke rera taken kasarsu gabanin soma fafatwar.

Kasar Italy ce dai ta lashe kofin bayan da suka tashi wasa 1-1 sannan aka tafi bugun fanareti kuma Ingila sukayi rashin nasara daci 3-2 bayan da wasu daga cikin ‘yan wasan kasar suka kasa cin fanaretin.

Duk da haka bayan tashi daga wasan magoya bayan kasar sun nuna wariyar launin fata ga wasu daga cikin ‘yan wasan kasar da suka hada da Marcus Rashford da Bukayo Saka da kuma Jadon Sancho, wadanda suka zubar da fanaretin.

Hakan kuma yasa mutane da dama da suka hada da kociyan tawagar da kuma fira ministan kasar sukayi Alla-wadai da halayyar magoya bayan sanna  sukayi kira da hukumomi su hukunta duk wanda aka kama.

Mai koyar ta tawagar kwallon kafar kasar, Gareth Southgate ya soki masu nunawa ‘yan wasan kasar wariyar launin fata sannan ya koka da kalaman wariyar da wasu daga cikin ‘yan wasansa suka fuskanta ya yin wasansu da suka yi rashin nasara a hannun kasar Italy.

A cewar Southgate nuna wariya ba dabi’a ce da ta dace da masoya kwallo kafa ba, a domin haka dole ne a dauki matakin ladabtar da wadanda ke da hannu a cin mutuncin ‘yan wasan guda uku.

Wasu daga cikin ‘yan wasan Ingila da suka kunshi Marcus Rashford da Jadon Sancho da Bukayo Saka sun gamu da wariyar ne a shafukan sada zumunta, bayan rashin nasararsu a bugun fenaretin da aka yi tsakanin Ingila da Italy wanda Italy ta doke tawagar tare da lashe kofin na Euro 2020.

Amma duk da yadda wasu daidaiku ke ci gaba da furta kalaman wariya da na cin mutunci ga ‘yan wasan 3, kocin na Ingila ya basu kwarin gwiwar tunkarar kowanne kalubale, ya yinda a bangare guda dan wasa Jude Bellingham ya wallafa hoton ‘yan wasan uku a shafinsa tare da rubutu a kasa da ke cewa munyi nasara tare haka zalika rashin nasara tare.

Shima Firamninistan birtaniya, Boris Johnson da hukumar kwallon kafar kasar sunyi tir da wariyar ya yinda jami’an tsaro ke ci gaba da bincike domin gano masu hannu a ciki da nufin hukunta su.

Shugabannin siyasa da kuma na bangaren kwallon kafar Birtaniya sun bayyana bacin ran su da cin zarafi da kuma nuna wariyar jinsin da ake nunawa ‘yan wasan kasar guda uku bakaken fatar da suka barar da fenareti a karawar da Ingila tayi da Italia daren Lahadi, abinda ya sa kasar ta gaza lashe kofin Euro 2020.

shima Firaminista Boris Johnson ya gamu da suka saboda kin Allah wadai da yadda yaki nuna bacin ran sa da yadda wasu ke yiwa ‘yan wasan kasar ihu saboda yaki da nuna wariyar jinsi da suke yi kafin fara wasannin su.

Manajan Ingila Gareth Southgate ya ce abin takaici ne yadda aka dinga amfani da kafofin sada zumunta ana cin zarafin ‘Yan wasan da suka sadaukar da rayukan su daga ciki da wajen kasar.

Southgate ya ce kungiyar ta su ta zama wani dandalin hada kan jama’ar kasa ba tare da la’akari da inda mutane suka fito ba ko kuma manufar su sannan kuma da yawa daga cikin mutanen kasar suna tare da ‘yan wasan.

Boris Johnson ya bayyana Yan wasan da matsayin gwaraza wadanda ya dace a karrama amma ba cin zarafin su a kafofin sada zumunta ba, ya yin da Firaministan ya ce abin kunya ne ga masu sukar su.

Kafin dai wannan lokaci Firaministan Johnson da ‘yan Jam’iyyar sa sun kare masu sukar ‘yan wasan saboda durkusawar da suke kafin fara wasa domin yaki da wariyar jinsi, inda yake kare masu musu ihu cewar suna da ‘yancin fadin albarkacin bakin su.

Tsohon dan wasan Manchester United, Gary Nebille ya zargi Firaministan da goyan bayan nuna wariyar jinsi lokacin da ya bayyana matan Musulmin dake sanya hijabi a matsayin akwatin gidan waya.

Facebook ya bayyana share kalamun cin zarafin da wasu suka yiwa ‘yan wasa ta kafar sa da kuma rufe shafunan sannan rundunar ‘yan Sandan London sun tabbatar da kaddamar da bincike akan lamarin, ya yin da hukumar kwallon kafar turai ta bi sahun masu sukar cin zarafin da kuma bayyana goyan bayan ta ga ‘yan wasan da hukumar Ingila.

Shi ma Yarima William wanda shine shugaban hukumar kwallon kafar kasar da uwargidan sa Kate da dan su George da suka kalli wasan ya bayyana bacin ran sa da cin zarafin da aka yiwa ‘yan wasan.

Exit mobile version