Euro 2020: Ronaldo Na Dab Da Lashe Takalmin Zinare

Ronaldo

Watakila dan wasan tawagar kasar Portugal, Cristiano Ronaldo ya lashe kyautar takalmin zinare a gasar cin kofin nahiyar Turai ta Euro 2020 a matakin wanda ya fi cin kwallaye a wasannin.

Koda yake an yi waje da Portugal mai rike da kofin a karawar zagaye na biyu, bayan da Belgium ta doke ta da ci 1-0 ranar 27 ga watan Yunin 2021 dan wasan na Jubentus ya ci Hungary kwallo biyu da Faransa da itama ya ci biyu da kuma Jamus da ya zura daya a raga,. jumulla guda biyar a karawar cikin rukuni kenan.

Dan kwallon Jamhuriyar Czech, Patrik Schick shima yana da kwallaye biyar a raga a Euro 2020, sai dai Ronaldo na gabansa kasancewar ya bai wa Diogo Jota kwallo ya zura a ragar Jamus.

Kawo yanzu kamar yadda aka fitar da Ronaldo daga gasar bana, haka shima Schick ya yi ban kwana da wasannin Euro 2020 sai dai akwai ‘yan wasan da suka ci kwallo hur hudu da suka hada da Romelu Lukaku na Belgium da Karim Benzema na Faransa da dan wasan Sweden Emil Forsberg, wadanda sun dade da komawa gida.

Gasar ta bana ta kai karawar daf da karshe, kuma ‘yan kwallo uku ne suka zura uku-uku a raga da suka kai wasan daf da karshen da suka hada da Raheem Sterling na Ingila da kuma Harry Kane da Kasper Dolberg na tawagar Denmark.

Hakan dama ce da wani daga cikin ‘yan wasan nan su kamo Ronaldo, ko su haura shi a yawan cin kwallo a gasar bana, tunda wani ko wasu daga ciki sai sun kai karawar karshe sannan ranar Lahadi za’a kece raini  a wasan karshe a filin wasa na Wembley.

Exit mobile version