Faɗan Matasa Na Ƙungiyar Asiri Ta Salwantar Da Rayukan Mutum 5

Daga A. A. Masagala, Benin

A cikin makon da ya gabata ne ‘ya’yan ƙungiyoyin asiri na matasa guda biyu da basa ga maciji a tsakaninsu, suka gwabza tsakaninsu sakamaon hakan ya mutum biyar suka rigamu gidan gaskiya, wato ƙungiyar da ta ke amsa sunar “Bikings” da kuma mai suna “Skylow” matsalar gaba da ke tsakaninsu ya sha haddasatashin hankali a garin Kalaba ta jihar Kurosriba duk da irin matakan tsaro da hukumar ‘yansanda a jihar ta ke ɗauka na kada fitinar irin wannan ta ci gaba.

A cikin waɗanda suka rasu ta sanadiyyar wannan faɗar akwai wani ɗan takarar muƙamin kansila sai kuma wani daga cikin ‘yan ƙungiyar asirin mai suna Mesembe wanda ‘yan ƙungiyar asiri na skylow suka yi wa kwanton ɓauna su ka kasha. Kuma irin wannan ya sha faruwa inda ƙungiyoyin suke kaiwa juna hare-hare na-sari-ka noƙe a lokuta daban daban.

Advertisements

Bayani sun nuna cewa, tun kwanaki kaɗan kafin hakan ya faru wata ƙungiya mai suna Scorpion da Skylow su ke take take na neman yadda za su aukawa ‘yan ƙungiyar asiri ta Bikings domin ɗaukar fansa a kan zargin da suka yi wa ‘ya’yan ɗayar ƙungiyar cewa, sune suka kashe musu wani jigo na ƙungiyarsu da ake ce masa Ecomuc.

A ɓangaren hukumar ‘yansandan jihar kuma, kakakin rundunar Irene Ugbo ta tabbatar da aukuwar lamarin amma sai dai tace mutum guda ne ya rasa ransa kuma ba ta yi wani ƙarin bayani ba.

 

Exit mobile version