FAAN Ta Samu Raguwar Haraji Da Kimanin Naira Biliyan 16

Hukumar kula da tasoshin jiragen sama a Nijeriya (FAAN) ta bayyana karin kudade ga fashinjojin, domin ta rage yawan gibin harajin da ta samu na naira biliyan 16, a cikin kasuwancin zirga-zirga na wasu watanni.
Shugaban hukumar FAAN, Capt. Rabiu Yadudu shi ya bayyana hakan a Abuja ranar Alhamis. Ya yi bayanin cewa, tun daga farkon watan Satumbar shekarar 2020, fasinjojin za su biya karin Naira 2,000. Yadudu ya kara dea cewa, hukumar FAAN ba ta kara wa fasinjoji karin kudade ba tun a shekarar 2011. Ya ce, an samu wannan kari ne sakamakon matsalolin da suka afku na hauhawan kayayyakin wanda babban bankkin Nijeriya ya kara kashi 12.82 daga cikin canjin Dala da ake saya a baya.
“Bayan haka, a shekarar 2019, ana canjin Dala a kan naira 344, amma a yanzu an samu kari sosai a cikin harkokin kasuwan canji a tsakanin naira da dala.”
Ya ce, gwamnatin tarayya ta bai wa hukumar FAAN da ta kara kashi 40 daga shekarar 2021, amma dai a yanzu ta kare, wannan ne ya haddasa wa hukumar samun faduwar kudaden shiga na naira biliyan 16.
“Sakamakon haka ne ya sa aka kara wa fasinjoji kari daga naira 1,000 zuwa naira 2,000 ga kowani fasinja. Wannan garambawul zai fara aiki ne a ranar 1 ga watan Satunbar shekarar 2020, wanda tuni hukumar da tattauna da kamfanonin jiragen sama da ke cikin kasar nan,” in ji Yadudu.
Ya ci gaba da cewa, muna kira ga dukkan masu ruwa da tsaki da masu amfani da filiyen jiragen saman da kuma sauran mutane da su bi wannan hukunci da hukumar FAAN ta zartar na wannan kari.
Ya yi kira ga daukacin fasinjojin jiragen sama da su yi kokari wajen sabawa da wannan karin domin ya zama dole sai hukumar ta yi hakan. Ya ce, yin wannan karin ba shi zai tabbata ba, za a iya sauko da shi idan akwai bukatar yin hakan a nan gaba.
Ya kara da cewa, yana da kyau fasinjoji su fahimci cewa, a cikin kasuwanci idan aka samu hauhawan abubuwa, to dole a bukaci yin farin farashi.

Exit mobile version