Kocin kungiyar kwallon kafa ta Liverpool, Jurgen Kloop, ya ce yana fatan Fabinho zai murmure ya kuma buga wa kungiyar wasan Premier League da za ta fafata da kungiyar kwallon kafa ta Manchester City.
Liverpool za ta karbi bakuncin Manchester City a wasan mako na 23 a gasar Premier League ranar 7 ga watan Fabrairu kuma Liverpool, wadda take ta hudu a kan teburi, ta ziyarci West Ham United a ranar Lahadi kuma ta samu nasara daci 3-0 a wasan mako na 21.
Fabinho, mai shekara 27, wanda ke buga tsakiya ya koma tsaron baya, sakamakon masu jinya da yawa da Liverpool ke fama da su sannan dan kwallon bai buga karawar da Liverpool ta doke Tottenham 3-1 ba, kuma bai yi wa Liverpool wasan da ta je West Ham ba.
Haka kuma dan wasan ba zai samu buga wa kungiyar ta Anfield wasan Premier da Brighton ba, daga nan ne Kloop ke sa ran Fabinho zai buga wasan da Liverpool za ta karbi bakuncin Manchester City.
Masu tsaron bayan Liverpool birgil ban Dijk da Joe Gomez na dogowar jinya a raunin da suka ci karo tun farko-farkon fara Premier League ta bana kuma hakan ne ya sa Liverpool ta mayar da Jordan Henderson mai tsaron baya daga tsakiya, inda take hada shi da wanda bai da kwarewa Nathaniel Philips mai shekara 23 ko kuma Rhys Williams mai shekara 19.
Nasarar cin Tottenham da Liverpool ta yi ya kawo karshen wasan Premier League da kungiyar Anfield ta buga ba tare da ta yi nasara ba duk da cewa Liverpool ce ke rike da kofin Premier League da ta lashe a bara, bayan ta kwashe shekara 30 tana fafutukar ganin ta lashe shi.