Connect with us

KIMIYYA

Facebook Na Kara Fuskantar Matsala Yayin Da Tsarin Aika Hotuna Cikin Sirri Na Masu Hulda Da Ita Miliyan 14 Ya Fuskanci Barazana

Published

on

Kanfanin Facebook ta tabbatar da cewa, matsalar data samu tattare da wani manhajarta mai suna “Glitch” ya sa masu hulda da ita fiye da Miliyan 14 sun samu matsala don kluma sakonnin da suke da nufin sa shi a tsalin sirri ya bayyana ga sauran jama’ar da basu yi niyyar su ga sakonin ba.
Wannan labarin ya kasance daya daga cikin hadili fallasa da kafar sada zumunci mafi girma a duniya ta shiga a ‘yan shekarun nan a tattare da tsarinta na sirrinta bayanan da masu hulda da ita ke bayyana wa ga abokansu, a baya Facebook ta fuskanci matsalar kutse da aka yi wa Miliyoyin masu amfani da ita da kuma badakalar rarraba DATA tsakaninta da wasu kanfanin kera wayoyin smartphone.
A sanarwar daya fitar, Mista Erin Egan, shugaban tsarin tabbatar da sirri na kanfanin facebook ya bayyana cewa, “Mun gano cewar, wasu sakoninb da ake da nufin aikasu a sirrance sun kasace a bayyanane ga sauran al’umma ba tare da saninsu ba sakamakon matsalar da muka samu na manhajarmu.”
Kanfanin na Facebook ya ci gaba da cewa, wannan matsalar ya shafi sakonnin da aka aika ne tdsakanin ranan 18 ga watan Mayu zuwa ranar 27 ga watan Mayu, a dai dai lokacin da kanfanin ke aiwatar da wani sabon tsarin rarraba sakonni musammam hotuna.
Wannan matsalar ta sanya yayin da mutum ya aika sako da nufin ya je a sirrance ga abokan huldanka kawai, sai kawai sakonnin ya bayyana ga jama’a baki daya.
“Daga yau muna sanar da duk wanda ya aika sakonni a dan tsakanin lokacin da muke magana daya sake duba tsarin da yake amfani dasu ya kuma duba sakonnin daya aika a tsakanin wannan lokacin” inji Egan.
“Muna kuma sanar da cewan wannan matsalar bai shafi sukkan sakonnnin da mutum ya aika kafin lokacin da muka bayyana a sama ba, ya kuma su iya ci gaba da amfani da farfajiyar Facebook ba tare da wani fargaba ba kamar dai yadda suke yi tun da farko, muna kuma mika sakon ba hakuri ga dimbin jama’a a kan wannan kuskuren da muka yi”
Kanfanin Facebook ya tabbatar da cewa, kanfanin kasar Chaina mai suna Huawei, wanda rundunar sojojin Amura ta haramra wa harkar Intanet saboda hannun ta a kan wasu badakalar kutse a kan hanyar sadarwa intanet a lokuttan baya, suna cikin wadanda aka bai wa lasisin na’aurar data samu matsalar, shirn hadakar tsakaninsu kuma ya yi shekaru.
Facebook ta ce, yarjejeniyar data kulla da kanfanonin kera na’aura fiye da 60 ya taimaka mata samun karin abokan hulda a kafafen sada zumunci.
‘yan majalisar dokokin Amurka sun nuna bacin ransu a kan yadda aka bai wa kanfafnoni kasar Chaina daman shiga hulda da bayanan jama’a a daidai lokacin da jami’ai a kasar Amurka ke neman hanyoyin kange Chaina daga shiga harkar sadarwar Amurka saboda dalilan tsaron kasa. Wannan badakalar ya zo ne makwanni da shugaban kanfanin Facebook, Mista Mark Zuckerberg, ya fuskanci tambayoyi mai tsanani daga ‘yan majalisun Amurka a kan yadda aka yi kutse a kan bayaan sirrin murane fiye da Miliyan 87 da ake zargin kanfanin “Cambridge Analytica,”, kanfani daya yi aiki da kungiyar yakin neman
Advertisement

labarai

%d bloggers like this: