Connect with us

KIMIYYA

Facebook Ya Kulle Asusun Bogi Miliyan 583

Published

on

Hukumar kafanin Facebook ta kulle asusu fiye 583 na bogi a cikin wata uku na farkon wannan shekarar ta 2018, kamar yadda kanfanin ta bayyana ranar Talata, ta kuma yi bayani dalla dalla hanyoyin data yi amfani dasu wajen tabbatar da kulle asusun da kuma tsaftace farfajiyar daga sakonnin badala da hotunan batsa da sakonnin yan tadda da kalaman batanci.

Da yake mayar da martani bayan jama’a sun bukaci a canza salo tun bayan fallasar nan ta “Cambridge Analytica data pribacy scandal” hukumar ta Facebook ta kuma kara da cewa, wadannan asusun da aka kulle koma bayan datse miliyoyin kokarin da ake yi na bude asusun bogi a kowanne rana.

Duk da haka, kanfanin na Facebook ya bayyana cewar, kashi 3 zuwa 4 na asusun da ake dasu a halin yanzu na bogi ne.

Sun kuma kara bayyana cewa, sun gano kashi 100 na sakonnin batanci da kuma fitar da sakonni fiye na Miliyan 837 da suka hade da sakonnin batanci a tsakanin lokacin da ake magana.

Haka kuma Facebook ta bayar da gargadi har sau Miliyan 30 ga sakonnin da suka kunshi tsirayci da hotunan tashin hankali da farfagandan yan ta’adda da kalamam batanci a lokacin da muke nagana.

Ingantacciyar hanyar kimiyya ta taimaka aiki a kan sakonni fiye da Miliyan  3.4 dake kunshe da hotunan ta’addaci a kashin farko na wannan shekarar fiye da abin da aka yi a shekarar 2017.

Kashi 85.6 na matsalolin, Facebook ne da kanta ke ganowa kafin masu amfani su sanar da hukumar gudanarwa, inji rahoton, wanda aka fitar kwana daya da dakatar da wasu manhaja 200 da aka fahinci suna karya dokar data shafi sirri da bayanan masy amfani da farfajiyar ta Facebook.

Wadannan akaluman ya yi daidai da 0.22 da kuma kashi 0.27 na gaba daya abin da masu amfani da Facebook fiye da Biliyan 2 suka gani tsakanin katan Janauru zuwa Maris.

“Abin nufi a nan shi ne, a duk abubuwa dubu 10,000 da aka kalla to akwai akalla kashi 22 zuwa 27 na hotunan tashin hankali,” inji rahoton.

Hanyoyin mayar da martani ga karya doka sun hada da fitar da mutum kai tsaye, da gargadi a India mutum yabsanya hotuna masu Tatar da hankali,ga wasu kuma da suka Katya dokar Facebook ana iya Samar da jamian tsaro musamman a inda lamarin ya shafi barazana ga rayuwa wani ko wata.”.

Ingantacciyar hanyar kimiyya da fasaha ya taimaka dakile da daukar mataki a kan sakonni fiye da Miliyan 1.9 dake kushe da farfagandar yan tadda, wannan nasarar ya karu da kashi 73 a kan abin da ake samu a shekarun baya, domin kuwa dukkannisu anyi maganinsu ne kafin ma a sanar da aukuwarsu, inji kanfanin.

Sun kuma danfanta wannan nasarar da amfami da kimiyyar nan mai gano halin da hotuna suke na “photo detection technology”.

Gano kalaman batanci nada matukar wahala ta hanyar amfani da naura, sai dai ana gano kalaman nuna banbanci da matsanancin kalaman ta hanyar lura da wadanda aka aika kalaman garesu.

“Dolw sai dan adam kawai zai iya gane wasu kalamai masu sarkakaiya da ake amfani dasu domin cin mutumcin wasu mutane.” Inji rahoto

Hukumar Facebook nada nufin samar da kariya da mutuntuta juna tsakanin masu amfami da ita.

Haka kuma Facebook ta dauki mataki a kan kalaman batanci har guda Miliyan 2.5 a tsakanin lokacin da muke bayani abin dake nuna karuwar kashi 56 a tsakanin watan Oktoba da Disamba.

Amma kashi 38 ne kawai kokarin Facebook ya bayyanar dasu sauran kuma masu karatune auka ankarar hukumar domin daukar mataki.

Sakonnin da suka fi dauke hankalin masu amfani da Facebook a wannan lokacin sun hada da hotunan dake dauke da tsitayci dana batsa, banda hotunan batsa na yara domin rahoton bai yi nazarinsu ba.

Bayanin ya kuma nuna cewa, an yi aiki akan sakonni Miliyan 21 a tsakanin watan Oktoba zuwa Disamba na shekarar 2017.

Wannan yana kasa da kashi 0.1 na hotunan da aka kalla da suka hada da bidio da sauransu.

An zargi Facebook da cire hotuna a wasu lokutta ma hotuna ne da dokokin kanfanin ta amince da amfani dasu, a in dake kawo bacin rai daga masu amfani da Facebook.

A watan Maris, Facebook ta bayar da hakuri saboda cire wani hoton talla dake nuna wani shahararren mai zanen nan dan kasa Faransa mai suna Eugene Delacroid, wanda hoton ke dauke da hoton wata mata da nononta ke a waje.

Shugaban hukumar Facebook, Monika Bicket, ya ce, hukumar na shirin daukan maaikata fiye da 3,000 domin tabbatar da tafiya da aiki a gurabe 7,500 a wannan shekarar.
Advertisement

labarai

%d bloggers like this: