Connect with us

KIMIYYA

Facebook Zai Gina Rumbun Bayani Na Dala Biliyan Daya A Singapore

Published

on

A ranar Alhamis ne kanfanin Facebook ta bayyana cewa, za ta zuba jarin Dala Biliyan wajen gina babbar rumbun bayanai a kasar Singapore, wannan runbun bayanai zai kasance na farko a nahiyar Asiya, za kuma a yi amfami da makamashi na musammam ne wajen tafiyar da runbun bayanan.
Ana saran cibiyar zai fara aiki gadangadan a cikin shekarar 2022, daga nan ne sakonnin Facebook zai rinka tafiya bangarorin nahiyar, kamar dai yadda Thomas Furlong, mataimakin Shugaban kanfanin Facebook ya bayyana wa manema labarai.
An shirya gina cibiyar ne a kan fili mai fadin kadada 170,000, za kuma a gina katafaren gini ne mai hawa 11 wanda zai iya jure dukkan yanayi musamman irin yanayin da aka fi samu a nahiyar Asiya, in da a kan samu yanayin ya kan kai 25 ‘degrees Celsius’ (77 Fahrenheit).
Za kuma a samar da na’urorin sanyaya dakuma na zamani da sauran kayyaki na zamani don tafiyar da cibiyar.
Wannan ita ce za ta kasance cibiyar rumbun bayanai na Facebook na 15 a fadin duniya.
Furlong ya kuma kara da cewa, Facebook, na da mutum Biliyan 2.23 masu amfani da shafinta na facebook a duk wata, a wata kididdigar da a ka gudanar a watar Yuni na wannan shekarar, an kuma zabi kasar Singapore ne saboda kasancewarta kasar mai kayyayakin aiki da kwararrun ma’aikata da kuma gwamnati mai saukin gudanar da hulda da ‘yan kasuwa.
Tuni kanfanin Google ta gina cibiyar rumbun bayanai guda 2 a kasar, tana kuma shirin gina cibiya ta 3, abin da zai kai jarin da kanfanin ta zuba zuwa Dala Miliyan 850.
Duk da kasancewar facebook nada tasiri a tsakanin jama’ar nahiyar Asya, jama’a da dama na sukanta musamman a kasar Myanmar saboda a cikinta ne masu tsatsarrar ra’ayi ‘yan kabilar Buddhist suke yada kalaman batanci a kan Musulmai ‘yan kabilar Rohingya marasa rinjaye.
Advertisement

labarai

%d bloggers like this: