Ibrahim Muhammad" />

‘’Fadada Kasuwanci Zai Taimakawa Samar Wa Matasa Aikin Yi’’

Kasuwanci

An yi kira ga yan kasuwa akan idan suka sami dama su rika kokarin fadada harkokinsu domin zai bada damar cigaba da baiwa matasa damar koyon yin harkar kasuwanci dan dogaro dakai.

Shugaban sabon Katafaren Shagon saida kayayyakin amfanin gida na girke-girken mata mai suna “Bin Mustapha Plastic” dake kasuwar Wambai, Alhaji Abubakar Kabir Indabawa ya yi wannan kiran yayin bude shagon a ranar Laraba.

Ya ce dama shagon na “Bin Mustapha Plastic and Kitchen” sun dade suna burin su samar dashi, sai yanzu Allah ya nufa aka bude don fara sana’ar kasuwanci musamman na kaya da suka danganci na bukatar Amare  da kawata gida a fannin girki.

Ya ce kara da cewa yawanci kayan da suka samar na  waje ne amma duk da haka suna da wani sashen da suke sai da wadanda ake a kasarnan kuma sun samar da shago ne don zamanantar da yanayin kasuwanci.

Alhaji Abubakar Kabir Indabawa ya ce, shi harkar kasuwa abu ne da take bukatar mutukar hakuri domin a rayuwama kacokaf hakuri shi yake kai mutum inda zai je balle kasuwanci ko menene yanayi in ya zo akayi hakuri dashi sai aga an sami abinda muke bukata.

Ya ce harkar da suke gaba daya ta iyaye ce domin su za su aurar da ‘ya’ya mazaje kuma su suke sabunta dakunan iyalai kuma sabon wajen e da suka yi tanadii na saukakawa.

Ya kara da cewa suna da ma’aikata da suka kai guda 10 wanda suna da burin kara yawansu anan  gaba, don haka zai taimakawa samawa matasa aiki. Saboda haka masu hali su rika bude wani wajen kara bude wani wajen zai taimakawa al’umma ya kuma taimakawa kai da makota daka samu domin za su iya samun alkhairi saboda zuwan ka.

Alhaji Abubakar Kabir ya jaddada kira ga masu hali su rika bude masana’anta musamman a irin wannan yanayi da take ciki.Ya godewa dinbin al’umma da suka zo na nesa dana kusa don tayasu  murna aka zo aka bude waje lafiya. Cikin manyan yan kasuwa da suka albarkaci bude shagon na Bin Mustapha Plastic and Kitchen shugaban rukunin kantunan ELSAMAD da shima ya yi fatan alkhairi ga mamallakin sabon kantin.

Shima Tsohon kakakin hukumar yansanda na Kano Magaji Musa Majiya ya yi fatan albarka a jawabin da ya gabatar a wajen taron.

 

Exit mobile version