Fadan Sudan Ya Hana Kananan Yara Samun Ilimi —UNICEF
  • English
  • Business News
Wednesday, October 8, 2025
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Fadan Sudan Ya Hana Kananan Yara Samun Ilimi —UNICEF

bySadiq
2 years ago
Sudan

Asusun Kula da Kananan Yara na Majalisar Dinkin Duniya (UNICEF), ya ce yakin Sudan ya raba akalla yara 450,000 da gidajensu, tare da haddasa gudun hijira zuwa kasashe makwabta.

Kungiyoyin ba da agaji sun ce ana hana wadannan yaran ‘yan gudun hijira ilimi, tare da fuskantar hatsarin fadawa hannun bata gari, kamar auren yara ko daukar makami don shiga kungiyar ‘yan ta’adda.

  • Kwana 5 Ga Rantsuwa: Waiwaye Kan Rawar Da Matan Shugabannin Kasa Suka Taka A Baya
  • Biden Ya Turo Tawaga Don Halartar Rantsar Da Tinubu

Yayin da dubun dubatan ‘yan gudun hijira ke isa kan iyakar Sudan zuwa Chadi, yawancin taimakon da Majalisar Dinkin Duniya ke bayarwa da kungiyoyin agaji ya mayar da hankali ne kan ruwa da abinci da kuma sauran kayan amfani na yau da kullum ga ‘yan gudun hijira.

Amma ‘yan gudun hijira kamar Abdelnasser Mahamout mai shekaru 18 da haihuwa, sun ce akwai matukar bukatar ilimi.

Yakin basasar Sudan, wanda ya fara a ranar 15 ga Afrilu, ya haifar da rikicin kabilanci a yammacin Darfur.

Dole ta sa ya gudu zuwa Chadi ba tare da iyayensa ba.

Mahamout ya ce tun makonni bai ji daga iyayensa ba, kuma ba shi da masaniyar suna raye ko sun mutu.

Yanzu haka yana zaune a wani karamin sansani tare da ’yan uwansa, kuma ya ce babu wata hanya da zai iya daukar jarabawar shiga Jami’ar Sudan.

Malek Mohammed, malami da ya yi gudun hijira zuwa kasar Chadi daga yammacin Darfur, ya koka da halin kunci da yaran da ya ke koyarwa a baya suke zama a ciki.

Mohammed ya ce malamai na kokarin samar da hanyar da yara za su yi jarabawar Sudan a Chadi.

Gwamnati a Khartoum ta daina aiki tun lokacin da aka fara yakin basasa, don haka da alama ba za a iya daidaitawa ba.

Education Cannot Wait, ECW, ita ce asusun Majalisar Dinkin Duniya don ilimi a lokutan rikici.

Daraktar kungiyar, Yasmine Sherif, ta kai ziyara kasar Chadi a watan Mayu, inda ta yi alkawarin bai wa kasar Chadi dala miliyan uku domin samar da ilimi.

Tasirin yakin Sudan kan yara bai takaita ga ilimi ba kadai.

Majalisar Dinkin Duniya ta sanar a ranar 12 ga watan Mayu cewa, wata masana’anta ta Sudan da ke samar da kashi 60 cikin 100 na abinci na musamman da ake amfani da su wajen magance matsalar karancin abinci mai gina jiki a kasar an lalata su saboda fadan.

Dubun dubatar yara a Sudan ne za su samu kansu cikin irin wannan hali.

ShareTweetSendShare

MASU ALAKA

Isra’ila Ta Kashe Falasɗinawa Sama Da 66,000 A Gaza Cikin Shekaru 2 – Rahoto
Kasashen Ketare

Isra’ila Ta Kashe Falasɗinawa Sama Da 66,000 A Gaza Cikin Shekaru 2 – Rahoto

October 7, 2025
Me Yarjejeniyar Kawo Karshen Yakin Gaza Da Amurka Ta Tsara Ta Kunsa?
Kasashen Ketare

Me Yarjejeniyar Kawo Karshen Yakin Gaza Da Amurka Ta Tsara Ta Kunsa?

October 4, 2025
Wadanne Kasashen Afirka Ne Ba Sa Goyon Bayan Kafa Kasar Falasdinawa?
Kasashen Ketare

Wadanne Kasashen Afirka Ne Ba Sa Goyon Bayan Kafa Kasar Falasdinawa?

September 28, 2025
Next Post
LEADERSHIP Da CMG Sun Karfafa Dangantakar Aiki A Tsakaninsu

LEADERSHIP Da CMG Sun Karfafa Dangantakar Aiki A Tsakaninsu

LABARAI MASU NASABA

Kasar Sin Ta Yi Kira Ga Kasashen Duniya Su Hada Hannu Wajen Raya Harkokin Mata

Kasar Sin Ta Yi Kira Ga Kasashen Duniya Su Hada Hannu Wajen Raya Harkokin Mata

October 7, 2025
Wakilin Sin Ya Ba Da Shawarwari Uku Kan Yaki Da Ta’addanci

Wakilin Sin Ya Ba Da Shawarwari Uku Kan Yaki Da Ta’addanci

October 7, 2025
Cika Shekaru 25 Da Kafuwa: ACF Ta Jadadda Kudirinta Na Samun Hadin Kai Da Zaman Lafiya

Cika Shekaru 25 Da Kafuwa: ACF Ta Jadadda Kudirinta Na Samun Hadin Kai Da Zaman Lafiya

October 7, 2025
Sauyin Yanayi: “Damfara” Ko Gudun Sauke Nauyi?

Sauyin Yanayi: “Damfara” Ko Gudun Sauke Nauyi?

October 7, 2025
SSANU, NASU Za Su Gudanar Da Zanga-zanga A Faɗin Nijeriya A Ranar 9 Ga Oktoba

SSANU, NASU Za Su Gudanar Da Zanga-zanga A Faɗin Nijeriya A Ranar 9 Ga Oktoba

October 7, 2025
Daukacin Mambobin Majalisar Kare Hakkokin Dan Adam Ta MDD Sun Amince Da Kudurin Da Kasar Sin Ta Gabatar Kan Kare Hakkokin Tattalin Arziki Da Zamantakewa Da Al’adu

Daukacin Mambobin Majalisar Kare Hakkokin Dan Adam Ta MDD Sun Amince Da Kudurin Da Kasar Sin Ta Gabatar Kan Kare Hakkokin Tattalin Arziki Da Zamantakewa Da Al’adu

October 7, 2025
Ɓatan-dabon Naira Tiriliyan 210: Kamfanin NNPCL Ya Buƙaci A Ƙara Masa Lokaci

Ɓatan-dabon Naira Tiriliyan 210: Kamfanin NNPCL Ya Buƙaci A Ƙara Masa Lokaci

October 7, 2025
Tinubu

Tinubu Ya Nemi Amincewar Majalisa Kan Karɓo Bashin Dala Biliyan $2.347 Da $500m Na Sukuk 

October 7, 2025
Cikar Wa’adin AGOA Ta Nuna Ra’ayin Amurka Kan Afirka

Cikar Wa’adin AGOA Ta Nuna Ra’ayin Amurka Kan Afirka

October 7, 2025
Da Ɗumi-ɗumi: Yakubu Ya Miƙa Ragamar INEC Ga Agbamuche-Mbu A Matsayin Shugabar Riƙo

Da Ɗumi-ɗumi: Yakubu Ya Miƙa Ragamar INEC Ga Agbamuche-Mbu A Matsayin Shugabar Riƙo

October 7, 2025

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

Exit mobile version