Daga Yusuf Shu’aibu,
Fadar shugaban kasa ta soki shugaban Cocin Katolika na Jihar Sakkwato, Matthew Kukah bisa “miyagun kalaman” da ya yi wa gwamnatin Shugaban Kasa Muhammadu Buhari, a ranar bikin ista.
A cikin kalamun Kukah na ranar Lahadi, ya yi kakkausan suka ga gwamnatin tarayya wacce shugaban kasa Buhari yake jagoranta sakamakon tabarbarewar tsaro a Nijeriya.
Ista dai biki ne wanda daukacin Kistocin duniya ke murnar gicciye Annabi Isa, wanda ake yi a duk ranar Juma’ar farko na watan Afrilu da kuma ranar Lahadi da Litinin din farkon watan Afrilu na kowacce shekara.
Da yake mayar da martani ga Kukah, mashawarcin shugaban kasa a kan fannin yada labarai, Garba Shehu ya bayyana cewa “kowane dan kasar nan yana da irin nasa ra’ayin, amma kuma gaskiya guda daya ce.
“Amma kuma duk mutumin da ke ikirarin shi mutumin Allah ne, kamar irin Mathew Hassan Kukah, to kada ya bari ya cusa son zuciya da rashin adalci idan zai bayyana gaskiya.
“Kukah ya bayyana wasu abubuwa da bag aske ba ne a cikin sakon da ya isar a lokacin bikin isata.
“Furucin da ya yi cewa ta’adancin Boko Haram a yanzu ya fi muni fiye da kafin gwamnatin Buhari ta hau karagar mulki a cikin shekarar 2015, ba magana ba ce da ta kamata a ce ta fito daga bakin mai ikirarin cewa shi malamin addini ba ne. Saboda haka Kukah ya je Barno ko Adamawa ya tambaye su ko akwai bambanci tsakanin shekarar 2014 da shekarar 2021. Bugu da kari, ya yin batun saka hijabi a Jihar Kwara kuwa, batu ne wanda kotun jiha ta bada hukunci. Kuma a wasu jihohi da dama tun zamanin mulkin Obasanjo ake fama da batutuwan, kuma babu inda sunan Buhari ya fito. Ko akwai ne?
“Kawai dai Kukah yana cusa siyasa ne, kuma yake kokarin jan shugaban kasa siyasar da shi ya riga ya ya afka a ciki.
“Gwamnatin da ta kafa ma’aikata guda musamman domin kulawa da masu gudun hijirar da suka rasa muhallinsu, ba za a zarge ta da laifin yin watsi da wadannan masu gudun hijira ba, kamar yadda Kukah ya yi zargi.
“Wasu kalaman Kukah fa ga su da kan gado wanda dama ya saba yi a duk inda a samu damar sakin bakinsa da bai iya yi wa linzamin da ya kamaci malaman addini su rika yi wa harshensu ba.
“Domin haka ne muke kira ga ‘yan kasa na-gari da su ci gaba da goyan bayan irin kokarin da gwamnati take wajen ceto kasar nan zuwa nmataki na gaba.”