Mujallar ta ce arzikin Dangote ya ragu daga dala biliyan 15.4 a shekarar 2016 zuwa biliyan 12.2 a bana. Hakan dai ya faru ne, a cewar Forbes, saboda faduwar darajar kudin Nijeriya.
Alhaji Dangote, wanda ya fi karfi a harkar siminti da sukari da filawa, ya ja hankalin duniya lokacin da ya ce yana son sayen kulob din Arsenal cikin shekara hudu masu zuwa.
A ranar Alhamis ne, Shugaban kamfanin Amazon Jeff Bezos ya maye gurbin Bill Gates na wani dan lokaci a matsayin mutumin da ya fi kowa arziki a duniya.