Bello Hamza" />

Faduwar Saraki: Fabrairu 23 Ranar ‘Yanta Kwara Ce -Lai Mohammed

Ministan Yada Labarai da Al’adu, Lai Mohammed, ya ce, a karkashin mulkin jam’iyyar APC za a dauki ranar 23 ga watan Fabrairu a matsayin ranar kwatar yanci ga al’ummar jihar Kwara.
”Ina mai bukatar gwamna mai jiran gado, da zaran an rantsar da shi a ranar 29 ga watan Mayu 2019, ya ayyana ranar 23 da watan Fabrairu (ranar da aka gudanar da zaben shugaban kasa da na ‘yan majalisa kasa) na kowannne shakara a matsayin ranar kwata yanci ga mutanen jihar Kwara,” Ministan wanda kuma yana daga cikin jagororin jam’iyyar APC a jihar Kwara ya bayyana haka ne a tataunawarsa da ‘yan jarida a garin Ilorin ranar Litinin.
Ya gode wa Allah da al’ummar jihar Kwara a bisa gaggarumin nasarar da aka samu a zaben da aka gudanar ranar Asabar a jihar, ya ce jam’iyar ta samu nasara a kan jami’iyyar PDP da ci 10 da 0, ya ce yana nufin sun ci PDP 10 babu ko daya, kama haka, an samu nasarar a kujerar shugaban kasa da kujerar sanatoci guda uku da kuma kujerar majalisar wakilai guda shida daga jihar.
”Sakamakon zaben da aka gudaanar a ranar Asabar yana nuna cewa, lallai jihar Kwara ta samu cikakken ‘yanci, yanci daga danniyar siyasa daga gungun mutane da suka mayar da al’ummar jihar Kwara a matsayin bayi, lallai Allah ya kawo mana karshen su, muna godiya ga Allah madaukakin Sarki” inji Mista Mohammed.
Ya kuma bayyana cewa, babu wani mutum shi kadai da zai dauki nauyin wanan nasarar da aka samu amma nasara ce da dukkan al’ummar ihar Kwara suka hada hanun samun sa, muna kuma godiya gaba daya.
Ministan ya kuma lura da cewa, bayan da aka dankara musu taken siyasa da ba a taba samu a tarihin jihar Kwara,sai ga shi al’umar jihar Kwara sun tattabar da bayanin da ake yi na cewa, karfin jama’a ya fi dukkanin karfin mutanen dake a kan karagar mulki gaba daya.
Ya kuma cewa, nasarar da jami’yyar APC ta samu a jihar Kwara yana kamar matsayin rushewar bangon Jamus da aka yi a shekarun baya ne, ya kuma bukaci a fito ranar 9 ga watan Maris don karasa rusa katangar gaba daya ta hanyar zabar sabon gwamna da ‘yan majalisarsa.
“An gudanar da sahihin zabe ba tare da labarin satar akwatin zabe ba, an kuma yi zabe a cikin natsuwa a dukkna fadin jhar hakan kuma koma bayan abin da ake samu ne a shekarun baya a jihar.”
Ya gode wa dukkan ‘yan jam’iyyar APC a dukkan fadin jihar tare da kuma dukkan al’ummar jihar a bisa hadin kan da suka bayar na nasara da aka samu dukkan mataki.
Ministan ya kuma bukaci yan jam’iyyar da su sake zage damtse tare da gayra dukkan kurakuran da suka yi a zaben da ya wuce don fitowa don bayar da gaggarumin kuri’u a zaben gwamna dake tafe a ranar Asabar na sama tare da zabar yan takarar kujerar majalisa na jam’iyyrar APC gaba daya.
Taron manema labaran ya samu halartar shugaban jam’iyyar APC na jihar Kwara, Hon. Bashir Bolarinwa da dan takarar gwamna na jam’iyyar Abdulrazak Abdulrahman da sanatoci guda biyu da aka zaba a ranar Asabar.

Exit mobile version