Fafaroma Ya Na Ziyara A Kasashen Larabawa

Fafaroma Francis ya na ziyara ta musamman a kasashen larabawa, wannan ziyarar ita ce ta farko da Fafaroman yake a yankin, akalla mabiya addinin kirista miliyan biyu ne suke rayuwa a yankin kasashen larabawan, ana sa ran Fafaroman zai yi jawabi a bainar jama’a ranar Lahadin nan mai zuwa, ana sa ran Fafaroman zai kai ziyara kasar Saudiyya ma.

‘Ina matukar farin ciki da Ubangiji ya bani damar kawo wannan ziyarar a yankin nan, sannan wannan wata dama ce ta kara samun cimma daidaito a tsakanin mabiya addinan Islama da na Kiristanci, don haka wannan ziyarar cike ta ke da tarihi.’ Inji Fafaroma Francis.

Fafaroman wanda ya fara jawabin shi da kalmomin sallama, wato Assalamu Alaikum, ya ce; imani da mahallici hadin kai yake kawowa ba rarrabuwar kawuka ba, duk muna da bambamce-bambamce, amma imanin yana kawar mana da kiyaya a zuciyoyin mu, sannan ya na samar da zaman lafiya a tsakanin mu.

Fafaroman zai yi kwana biyu a kasar hadaddiyar daular larabawa wato (UAE), akwai bambamci a tsakanin kasashen larabawa kan yarda al’ummar Kirista suke da ‘yancin guudanar da addininsu, ana sa ran halartar mutum 120,000 a yayin da Fafaroman zai gudanar da bikin ibadar Kirista a birnin Anu Dhabi a ranar 5 ga watan Fabrairu da muke ciki.

‘Yan rajin kare hakkin bil-adama da dama sun suki ziyarar Fafaroman, musamman da yake kasar UAE ta na kan gaba wajen jagorantar yaki kan al’ummar Yamen, inda wasu suke ganin ziyarar nan ta Fafaroma nuna goyon baya ce ga yakin da kasashen larabawan suke yi da al’ummar Yamen.

Exit mobile version