Fadila H. Aliyu Kurfi" />

Fagacin Katsina Alhaji Iro Maikano: Gwarzonmu Na Mako

Mai girma Fagacin Katsina kuma Hakimin Matazu, ALHAJI IRO MAIKANO, ya kasance dattijo hadimin al’ummarsa a masauratarsa da ke Matazu, jihar Katsina da ma Nijeriya bakidaya. Wannan dalili ya sanya tsakanin wakiliyarmu ta LEADERSHIP A YAU LAHADI, FADILA H. ALIYU KURFI yin tattaki har masarautar tasa, inda ta samu tattaunawa da shi kamar haka:

Ina so mu ji cikakken sunanka da nasabarka?

To, a’uzubillahi minashshaidanur rajim, sunana Ibrahim wanda a ke ce ma Iro a hausance, sunan mahaifina Abdullahi wanda shima ake cema sa Maikano saboda haka kin ga sunana ya kama Iro Maikano Matazu to kin ji wannan shine cikakken sunana.

 

Ina son na ji dan takaitaccen tarihinka da na Masarautar Matazu?

Tarihi na an haife ni a 20/4/1953, kamar yanda ake yi ga al’adar Bahaushe, mahaifiyata suna Katsina da mahaifina da za a haife ni aka koma goyon cikina a Funtuwa saboda mahaifiyata mutuniyar Funtuwa ce, so a Funtuwa aka haife ni, bayan haihuwata mun dawo garin Katsina inda anan na yi makaranta, na fara makaranta a (Iyatanci Primary School) makarantar Iyatanci itace za ki gani da shafen makuba din nan inda su Maigirma Sardaunan Sokoto da su Tafawa Balewa duk dai manyan Arewa kusan nan suka yi middle, to anan na yi Iyatanci aji daya zuwa aji ukku, a lokacinmu ida ka gama, (junior primary school) ka kan tafi (senior secondary school) bayan mun gama shekara ukku a karamin aji sai muka wuce (senior school) Kofar Sauri, lokacin akwai wasu a Dutsinma na kwana a Malumfashi duka na kwana ne, to sai  mu dai aka kai mu nan Kofar Sauri, da muka gama sai muka zo nan Probision Secondary School nan Katsina wacce ta koma Gobernment College Katsina a nan muka yi aji biyar a lokacinmu aji biyar ake yi, sai Allah ya taimake mu aka dauke mu babbar makarantar a shekararmu ce ta farko a lokacinmu aka tara duk higher schools, waccen ake ma HSC ana yi HSC kamar gobernment College Katsina ayi a gobernment college Kaduna, Barewa college anyi a Keffi ana yin HSC a higher schools. To da kanmu ne aka ce duk higher school su dawo abude makaranta a Zariya wato CAS Zariya 1973.

Mu ne na farko da muka bude makarantar Cas Zariya muka shekara biyu muka shiga Jami’a, ni a Jami’a na karanta fannin tattalin kudi ko ajiyar kudi BSC Accounting, lokacinmu rayuwa da sauki muna makaranta aka dauke mu aiki, manyan kamfanoni na duniya suka taru suka zo makarantu kana gama makaranta a daukeka aiki sai suka yi mana interbiew su daukeka ni an dauke ni a Liber Brothers. Saboda haka na je na yi bautar kasa a Cross Riber State, lokacin Cross Riber na tare da Akwaibom ne a hade, muka yi orientation a Oyo wacce take Akwaibom a yanzu kana muka je muka yi serbice a Cross Riber State a Calabar, muna gamawa ni ko gida ban dawo ba sai na wuce wurin aiki na Liber Brothers dama an dauke ni aiki, a cen na fara aiki kana daga nan na dawo gwamnatin jaha wurin da na yi higher school nan Cas na zama finance officer, nine  finance ofisa na farko ma, daga nan na koma Collage of Education Kafancen nine basa na farko, sai aka bude federal Polytechnics na farko guda shidda, Nasarawa, Kauran Namoda da sauransu sai aka dauke aka sake mayar da ni Kauran Namoda nine basa na farko a Kauran Namoda na zauna shekara biyar ko shidda cikin yardar ubangaji aka zo za’ayi kidaya ta Census kuma National Population Commission ta na son ma’aikata aka dauke ne a matsayin assistant director lebel 15, to muna nan mun kai kidaya a 1991 aka gama na zama deputy director da aka gama Census sai aka yi mani posting a ofishin accounter general of federation nan aka yi posting dina Ministry Of Defense to a ministry of defense anan na yi ritaya a 2013 cikin kaddarar ubangaji na ajiye aiki wannan shine takaitaccen tarihin karatuna da aikina.

 

Ranka ya dade, wacce shekara a ka ba ka sarauta da asalin nada ka?

An nada ni sarauta kamar shekara 26 da ta wuce yanzu, an nada ni a watan Yuni 1992. Ni ne Fagacin na farko da a ka nada, saboda lokacin a ka bayar da karamar hukuma a da Matazu da Musawa su na tare, da a ka cire Matazu daga cikin Musawa sai aka sa ni Hakimin Matazu, wato aka yi ma ni Fagacin Katsina. To, yanzu na yi shekaru kusan 20 da wani abu Ina sarauta da aka ban sarauta na so na ajiye aikin gwamnati to lokacin Janar Babangida ke mulki, da Babangida ya bayar da tabbaci na amshi sarauta amma kar inbar aiki saboda za mu yi census a 1991 ni kuma an nadani sarauta 1992, saboda haka yace ya yarda na amshi sarauta amma karnabar aikina to kuma haka Maimarta ba marigayi Dr Muhammadu Kabir Usman ya yarda cewa na cigaba da aikina, ina ga kamar nine Hakimi na farko da yana Hakimi kuma yana sarauta amma yanzu akwai kusan biyu da suka karayi na ga kamar ba yarda.

 

Matazu na ga kamar garin Fulani ne kuma yanzu kasa na cikin dan hatsaniya, saboda rikicin Fulani. Shin ko wannan gunduma taka na fuskantar irin wannan barazanar?

To bari in gyara maki kadan; Matazu ba garin Fulani ba ne…

 

(Dariya) Amma ranka ya dade na gan ku duk farare ne…

(Dariya) Mu mu ne Fulani, amma Matazu garin habe ne, mu kusan duk Fulanin da ke nan zuwa su ka yi. Matazu gari ne mai dumbin tarihi. Mu mun zo daga wani gari ne da ake cema Sanyina a kasar Sokoto, daga Sanyina kakannin iyayenmu suka taso suka zo kasar Katsina a takaitaccen sai Allah ya yi masu sarauta tare da Maimarta Sarkin Katsina Dikko tun yana Durbi wanda ya haifi kakanmu yana Muduru  magajin Muduru a lokacin wanda ake ba garin Muduru babban Dandurbi ne amma saboda aminci dake tsakanin Dikko da Maidamisa Sarkin Musawa Yero wanda ya haifi kakanmu sai aka yi masa Muduru shi kuma shi Dikko yana Durbi da Allah ya ba shi sarautar Katsina sai ya dauko kakanmu sai ya mai do shi Musawa.

Musawa lokacin babban dan Sarki Katsina Abubakar wanda aka cire aka ba Dikko shike sarauta sai aka mai da shi Tsaskiya, daga Tsaskiya wacce ta zama Safana sauran ya koma tarihi, garin fulani nan muna da fulani da dama, amma abubuwan da muke yi kullum muna hada kawunan mutane kamar Kwanan mun nada kwamiti-kwamiti kowanne Mai’unguwa mun ummurce shi, da ya je ya fidda mutane sahihai kamar mutum goma-goma wanda sune magabata ko kuma masu kula, masu ruwa da tsani na wannan unguwa, kamar shi Mai’unguwa Sarkin Noma Liman kamar samari kungiyar Youth kamar mata, Sarkin Fawa haka dai kamar mutum goma sune za su rika kula da abin da ke faruwa, duk sati su yi taro duk abinda suka tattauna ko suka gani su sanar da magajinsu, shi kuma duk sati zai zo da rahoton zaman da suka yi na tsaro, saboda haka fulaninmu nan kowanne wuri akwai Ardo wanda shine mai kula duka, sannan kuma akwai wasu fulani da ke kula da sauran fulanin, a takaice gaskiya ba mu da matsalar fulani da akan samu akai akai amma cikin yardar Allah anyi maganin wannan matsala ta fulani, fulaninmu zaunanni ne musansu sun sanmu kuma babban abin ba mu makwabtaka da manyan dazuzzuka irinsu dajin Rugu, rashin kusanci da manyan dazuzzuka ya kara tallafa mana.

 

Bisa sauraron tarihinka da na yi, ka yi ilimin boko sosai kuma ka yi aikin gwamnati. Na san za ka zamo mai kishi da sha’awar ganin an yi ilimi boko. Shin ko akwai wani taimako da ake yi ma mata a karamar hukumar nan kasancewar an ce matan Arewa ne koma baya ta bangaren ilimi?

Eh, gaskiya Ina yi. Mu na da makaranta ta Community Debelopment wanda mu muka gina ta mutane suka hadu aka gina makarantar ta mata ce zalla, saboda haka mata ke zuwa, a baya mai girma gwamna RT Honorable Aminu Bello Masari anan ya kaddamar da Girls Child Education na farko a Matazu saboda haka ana mayar da hankali sosai a wurin karatun mata, kilan baki san wannan ba, shi garin Matazu gari ne na ilimi da wuya ki wuce gida daya biyu baki samu mahaddaci ba, shi karatu an dauka wanda ya karanta ingilishi ko Faransi shine yayi karatu idan ka yi da Hausa ko wani yare baka yi karatu ba, gaskiya akwai wanda suka shahara cikin wannan gudduma ta mu kuma mata na taka kyakkyawar rawa.

 

Wacce zaburarwa za ka yi ma manyan gobe a kan neman ilimi da zama lafiya?

To, zamani ne yanzu kamar yanda nace maki mu tun kafin mu gama makaranta an dauke mu aiki babu masu karatun da yawa bare aiki yayi wahala, to amma yanzu ga makarantu nan Unibersity suna ta yaye dalibai da suka yi karatu kala-kala ni abinda zan ba da sha’awa samari su ko yi sana’a ko kasuwanci ba sai ka fara da manyan kudi ba, kar kace dole sai da babban jalli ga gwamnatin tarayya ta fito da hanyoyi daban-daban na taimakon matasa ya kamata yaranmu su tashu tsaye wajen koyon sana’ar hannu da abubuwan nan na entrepreneurship Alhamdulillahi matasa sun fara hada kansu sun fara koyama matasa sana’o’i daban-daban kira takalma man shafawa abubuwa da dama kala-kala. Babbar matsalarmu da muke da ita shine rashin wuta ko masana’anta duk inda ka yi masana’anta daya ko biyu ta ishi matasa ‘yan bokon da ke garin, amma babu wutar kwanaki an kamanta an yi wurin yin fenti, wurin kifi haka dai ga su anyi amma babu wutar. Sannan mun roki alfarma wurin mai girma gwamna anyi mana hanyoyi kasancewar ita kasar Matazu ta kowanne bangare ta yi iyaka da ruwa ne.

 

Wane fatan alkhairi za ka yi ma kasarmu Najeriya da kuma shi kansa mai girma shugaban kasa?

Kullum abinda muke kiran mutane akara hakuri ita banna tafi sauki akan gyara, idan aka baka gida aka ce ka rushe shi cikin minti biyar ka rusheshi, amma gina shi matakan na da yawa saboda haka  mutane su kara kokari komi lokaci gare shi, amma abu guda wanda ko wanene ya yi amanna da Buhari mutumin kirkine ba azzalumi bane, ansan duk abinda aka fada sai dai a fada ba cikin ana so ba da an kara hakuri komai zai zo da sauki an samo hanyar inganta abinci, rashin kudi an kawo hanyoyin da mutane kudi zai zo hannunsu, abubuwa da yawa wanda mutane ke koke da su gashi ana ta shawo kansu, amma mutane akara hakuri idan akwai yarda da amincewa da mutum ba zai cuceka ba ba zai saci kudinka ba da duk abinda yake yi sai ka kara hakuri, idan ana cutar mutum da wahala ya hakura amma duk wanda yasan Buhari a wannan tsawon lokacin halinsa dai ne ba siyasa ya fara ba, halinsa a soja an sani halinsa ma’aikacin gwamnati an sa ni, sai muce mutane su kara hakuri na kusa da shi sun san kokarin da yake yi, mu da ke da shekaru mun gani, karewar tattalin arzikin kasa 1993, amma duk za su zo wuce, mu dubi fa ba lokacin siyasa ba har lokacin mulkin sojoji barna aka yi ta yi ba a tanada komai ba, kudin ma neman ya za a bata su aje yi, lokacin Gowon cewa ake yi muna da kudi mararsa iyaka matsalarmu ba judi bace matsakarmu me za mu kashe sojoji ke nan lokacin haka siyasa, sai ace shekara ukku a canza shi a kara hakuri dai.

 

Exit mobile version