Tare da Sheikh Ibrahim Khalil
A aiko da tambaya ta wadannan imel: shafinfahimtafuska@yahoo.com ko nasirsgwangwazo@yahoo.com ko kuma sakon ‘tedt’ ta wannan lamba domin Malam ya amsa tambaya: 08096972247.
Salam. Malam, don Allah ina so a yi min karin bayani a kan wankan tsarki.
Wankan tsarki shi ne, wankan janaba ko wankan jinin biki ko wankan haila. A nan ana nufin kawai mutum ya wanke dukkanin jikinsa da ruwa, ya cuda ko’ina da ina a kafatanin jikinsa shi kenan ya yi wankan tsarki. Idan wankan janaba ne dukkanin jikinsa zai wanke da ruwa kamar yadda yake yin wanka, banbancin kawai shi wannan ba wankan sabulu ba ne. Sannan za ka iya yi da shawa ko kuma ka shiga cikin ruwa ka wanke ko’ina a jikinka. Haka ita ma mace duk wankan iri daya ne babu wani banbanci.
Assalam. Malam, idan ana bin mutum bashi sai wasu suka kashe shi misali kamar ‘yan fashi, za a biya masa wannan bashin ne ko kuwa alhakin bashin zai koma kan wadanda suka kashe shi?
A’a, ai idan mutum ya yi kisan kai abinda yake komawa kansa kadai shi ne zunuban wanda ya kashe. Idan mutum ya yi kisan kai, zunuban wanda ya kashe za su dawo kansa, amma hakkin da wani yake bin sa na bashi, dole sai ya biya ko dai ‘yan’uwansa su biya masa ko kuma a lahira a biya masa da ayyukansa na alheri. Amma zunuban wanda aka kashe shi ne yake koma wa kan wanda ya kashe shi.
Saboda haka, wajibi ne idan wanda ake bi bashi bai samu ya biya ba har ta Allah ta kasance ‘yan’uwansa ko iyayensa su biya masa. Babu maganar cewa don kashe shi a ka yi ko wani abu makamancin haka ba za a biya masa bashi ba, wannan nauyin na bashi yana nan a kansa tunda hakki ne na wani. Maganar kisan da aka yi masa kuma wannan shi ma wani abu ne daban mai zaman kansa, ma’ana dukkanin zunuban da wanda aka kashe din ya aikata, za su koma kan wadanda suka kashe shi kai tsaye.
Assalam. Malam, don Allah ina so na san ko akwai Nassi ko Hadisi da ya halatta yin Mauludin.
To, ala aiyu halin ita dai maganar Mauludi abu ne da aka fara yi shekaru dubu da suka gabata. Abin nufi a nan shi ne, an fara yin Mauludi a shekara ta dari hudu da wani abu bayan hijira, don haka yanzu kimanin shekaru dubu kenan.
Don haka abinda nake so a fahimta a nan shi ne, da wanda ya ce a yi Mauludi da kuma wanda ya ce ka da a yi, babu wani wanda ke da nassi ko nadisi, kadai kowannen su ya ginu ne a kan wata fahimta tasa, amma ba nassi ko nadisi ba. Wani fahimtarsa da kur’ani da hadisi da wadansu ka’idoji da kuma wasu dalilai ne yasa yake ganin bai kamata a yi Mauludi ba, wasu kuma fahimtarsu da kur’ani da hadisai da wasu ka’idoji ne yasa suke ganin ya halatta a yi Mauludin.
Misali, tunda Sallah Allah ne ya ce a yi ta, babu wata rigima a kan ta, haka tunda giya Allah ne ya haramta shan ta, nan ma babu wata rigima a kan shan ta, amma duk mas’alolin da babu nassi a kan su cewa a yi ko kada a yi, kowane bangare zai dogara ne da tunaninsa da kuma fahimtarsa.
Don haka, wanda yake yin Mauludi bai kamata ya kyamaci ko ya furta kakkausan lafazi a kan wanda ba ya yi ba, shi kuma wanda ba ya yi shi ma bai kamata ya fadi kakkausan magana ko lafazi a kan wanda yake yi ba. Wannan shi ne abin da ya kamata, ma’ana dai kowa ya yi kokarin tsayawa a matsayinsa.
A takaice dai, wanda yake yin Mauludi ba za a zo a hana shi dole ya daina yin Mauludin ba, wanda kuma baya yin Mauludin ba za a sa shi dole ya yi Mauludin ba. Amma da zarar wani ya fahimci wani ya fi shi hujja, shi kenan sai ya sakar masa babu wani abin tashin hankali. Saboda haka bai kamata wani ya yi wa wani gani-gani ba tunda dukkanin su a kan fahimta suke babu wani mai nassi ko hadisi.
Sai dai da yake dabi’a ta dan Adam, duk lokacin da ya dauki wani tunani ko fahimta, yana fifita ta a kan wata ne. Kamar jam’iyyar siyasa ce ko sayan tufafi ko abin hawa, duk lokacin da mutum ya zabi wani abu da ya yi masa, to yana fifita shi ne a kan wanin sa.