Assalamu Alaikum. Malam, ni ne nake zargin wani mutum da wata matar aure, zan iya fadawa mujinta?
Haramun ne ka fadawa mujinta, haramun ne ka fadawa wani kuma haramun ne ka bincika don tabbatar da gaskiyar al’amarin ko abin da ake yin zargin a kai din. Don haka babu ruwanka da yin wani bincike a kai, ko tattauna al’amarin tare da wani ko wani abu makamancin haka, kawai ka kyale su.
Allah Ya sakawa Malam da alheri. Wallahi ina da sha’awa sosai, sannan kuma aurena sai nan da shekaru biyu. Malam, me ya kamata na rika yi?
Abin da za ka rika yi shi ne, sanya lemon tsami a abicin da za ka ci. Kazalika, abin da ya sa kake jin haka, saboda sabuwar balaga ce da kuruciya; amma duk da haka kada ka damu za ka wuce wannan lokacin.
Assalam Malam. Don Allah a taimaka min, ina so na bar zina amma abin ya gagara na kasa dainawa, don girman Allah a taimake ni.
To, babban abin da ya kamata kuma hanya mafi sauki shi ne abu uku, na farko ka nace da yin ibada yadda ya kamata, ka tabbata cewa, Sallolin nan biyar kana yin su a jam’i, sannan ka rika zuwa minti ashirin ko sha biyar kafin a tayar da Sallah, ka yi nafila raka’a biyu ko hudu kafin Sallar azahar ko bayan an idar ko ka je Sallar la’asar ka yi Sallah raka’a biyu ko hudu kafin liman ya zo, ko ka je Sallar magriba minti talatin kafin liman ya zo ya kuma ci gaba da istigfari kafin liman ya zo, sannan bayan an idar da Sallar magriba din ka rika yin Nafila raka’a shida. Haka zalika, ka fin Sallar isha’i, ka je da wuri ka yi Sallar raka’a biyu, bayan an yi isha’I ka yi shafa’I da wuturi ko kuma ka yi nafila raka’a biyu idan ka je gida ka yi shafa’I da wuturin. Sallar asuba kuma ka je da wuri kafin a kira assalatu, mana’a dai ka jajirce wajen yin wadannan Salloli biyar a jam’i.
Abu na biyu kuma, ka ci gaba da jin cewa, abin da kake aikatawan nan ba daidai ba ne kuma ka rika jin haushin kanka da abokiyar zinan taka sannan ka rika rokon Allah gafara. Abu na uku kuma, ka yawaita yin ayyukan alheri, kamar azumi, sadaka da kyauta da sauran duk wani abu da ka san Allah yana so daidai gwargwadon ikonka, insha Allahu Allah zai yaye maka. Haka nan ka daure ka yi aure, idan z aka yi auren kuma ka auri irin matar da ka fi sha’awa.
Salam. Malam, don Allah idan mutum ya sa yi abu a hanya ya manta bai biya kudin ba, shi ma wanda ka sayi abun a wajen sa bai tuna ya tambaye ka kudin ba sai bayan ka yi gaba sannan ka tuna ka dawo amma ba ka same shi ba saboda yawo yake ga shi kuma ba Musulmi ba ne, Malam, ya kenan za ka yi da kudin?
Sai kawai ya yi masa sadaka da kudin, Allah Ya san ta inda zai mayar wa mai kudin kudinsa. Idan kuma daga baya sun hadu, ya mayar masa da kudinsa ladan sadakar kuma yawo wajensa.
Assalam. Malam, na kasance mai yawan yin sadaka da kyauta amma sau da dama maigidana yakan yawan yi min fada a kan hakan, Malam, idan nay i bai sani ba akwai matsala?
Idan da dukiyarsa kike yin wannan kyauta da sadaka tunda bay a so, ki daina yi masa kyauta da dukiyarsa, amma idan da dukiyarki kike yi, a nan dole za ki rage yi sosai ta yadda ba zai ji ba kuma ba zai rika gani ba. Idan kika yi haka babu shakka za a samu zaman lafiya a tsakanin ku.
Assalam Malam. Idan mutum ba shi da lafiya, ba zai iya azumi ba sai ciyarwa, maimakon ya ciyar da safe da yamma da kuma dare, zai iya bayar da kwanon masara ya wadatar, ko kuwa sai ya hada da kudin cefane?
A’a, mutum zai iya bayar da mudu daya na masara ko dawa ko gero ko wake ko kuma shinkafa mudu daya tak ba kwano ba kamar yadda wasu ke fada. Amma idan yana da hali babu laifi idan ya hada da kudin cefane.