Yusuf Kabiru" />

Fahimtar Masana Kan Bambancin Namiji Da Mace

Masana daga fannoni daban-daban sun bayyana ra’ayinsu kan yadda suke ganin bambancin namiji da mace. Ga wasu daga cikin irin wadannan ra’ayoyin:-

PLATO: Wani hamshakin masanin halayyar dan’adam ne. Ya yi fice kwarai a zamaninsa, saboda haka ake masa lakabi da Baban masana halayen dan’adam. A cikin littafinsa da ake kira; ‘Jamuhuriya’ ya fada cewa, mata da maza na da halayya mai kama da juna. Saboda haka mata za su iya yin duk abin da maza ke yi, har ma aikin soja da wasan guje-guje. Ba wani abu takamaime da namiji zai yi wanda mace ba za ta iya yi ba. Kodayake ya yarda da cewa ta gaza kadan a wajen tunani, amma ya kara da cewa duk bambamcin, a kan yawa ne ba a kan karko ba. 

ARISTOTLE: Shi kuma wannan dalibin Plato ne. Sai dai ra’ayinsa ya sha bamban da na Malaminsa. A cikin littafinsa da ake kira ‘siyasa,’ ya bayyana ra’ayinsa a game da bambancin. Wanda hakan ke nesantar da shi daga ra’ayin Malaminsa. Ya ce, bambancin bai tsaya kawai a kan yawa ba, amma har da karko. A ganinsa, aikin da yake jarumtaka ga namiji, bai cancanci yabo ba a wurin mace. 

PROFESSOR REEK: Wannan ba’amurke, wani masani ne a kan halayyar dan’adam. Ya shafe Shekaru da yawa yana bincikar matsayin mace da namiji. Shi ma ya bayyana bambance-bambance masu yawa a cikin littafinsa. Ya ce dalilin da ya sa mace ba za ta ita yin wasu abubuwa da Namiji ke yi ba, shi ne don Duniyarsu ba daya ba ce. Duk da suna da jiki daban da juna, kuma fahimtarsu daban ce, hanyar da suke dauka wajen maganin matsaloli daban ce. Bambance-bambancen ne, suke sa su zama wuri daya, da kaunatar juna, da rashin gajiya da juna. 

Farfesa Reek ya kara da cewa; namiji ba zai so a ce a kowane lokaci yana tare da mace ba, amma ita ba ta gajiya da ganin masoyinta. Ita mace a kullum nema take ta kara kyau, amma shi namiji, ba abin da ya dame shi da haka. Babbar kalmar da mace ke son ji ta fito daga bakin mijinta ita ne, “ina matukar sonki.” Shi kuma ba abin da zai faranta masa rai, kamar ta ce masa “Ina farin ciki da ji da kai.” 

Namiji mai tarayya (kusantar) mata da yawa, ya zamanto abin sha’awa a wajen mata. Amma macen da maza da mata suke tarayya da ita ta zamanto abin kyama ga maza. Nasara ga mace ba ta wuce mallakar zuciyar mijinta ba, shi ko namiji, a ce ya sami mutumci a idon jama’a. Burin namiji, shi ne ya iya juya ra’ayin matarsa zuwa ga abin da yake so, ita kuma wannan bai zama komai a gare ta ba. 

CLEO DALSON: Cleo, wata mace ce masaniyar halayen jama’a, wacce ta kware a kan sanin halayen jinsin mata tana cewa: “Mata ba za su tsaya su yi tunani wajen aiwatar da niyyarsu ba. Maza kuwa sai sun tantance, kafin su aiwatar. Muhimmin abu ga mace shi ne ta sami tsaro da kariya ta yadda za ta sami damar sheke ayarta, ba tare da muzgunawa ba, tana samun haka kuwa sai ta saduda. Duk abin da ya shafi dogon tunani na buwayarta.”

WILL DURANT: A cikin littafinsa ‘Jin dadin halayen jama’a’ yana cewa, bambance-bambancen, yana farawa ne a lokacin da dan’adam ya fara balaga. A nan ne soyayya da wasu halitta ke kara kunno kai; kamar su nono ga ‘ya mace, gashin gaba da na kirji ga namiji. Mace a wajen soyayya ta fi namiji wayo, don bukatarta na sha’awa kadan ne. Wannan ne ya sa idanuwanta ba sa rufewa a game da haka. 

Bayan haka a mataki na biyu ya ba da ra’ayin Stalin inda yake cewa, “a lokacin da mutum ya balaga, ba kawai kwan haihuwa kawai yake samarwa ba, amma da akwai wasu kwayoyin halitta da ke cikin jini, wanda ke sa kwakwalwa zurfin tunani, da kuma canjin halaye, ta hanyoyi dabam-daban. Roman Rolland na cewa: “Da akwai wasu shekaru a rayuwar mutum da canje-canje ke faruwa a hankali, sabbin tunani su cika shi, kamar neman sanin kwakwaf, sai dai kunya ta dan janyo shi baya. Shi namiji mai nema ne a kullum, don yakan iya bayyana soyayyarsa a fili, ba ya iya danne sha’awarsa. Son kyau da farin ciki yake sanya shi kawo mace a karkashinsa.

Wannan masanin halayyar dan’adam ya ci gaba da cewa: “Duk irin tsattsauran ra’ayin namiji, sai ka ga mace na iya juya shi, ta yadda abokanensa ba za su iya ba. Duk wannan na faruwa ne saboda irin hakuri da dauriyarta. Wannan kuma ke iya ba ta damar rarraba soyayyarta ga maza, ba tare da ta kawo hargitsi ba, kuma a tsawon lokaci. 

MUSSET:  Shi ma masanin halayyar dan’adam ne yana cewa; “wasu mazan makaryata ne, munafukai masu cin amana, wawaye masu girman kai. Su kuma mata suna da kunya, sai dai rashin tabbas. Ga su kuma ragwaye. Amma akwai abu daya da yake tsarkakke da muhimmanci, wannan abu kuwa shi ne haduwar wadannan kasassun halittu. Nokewa da (bayyana soyayya) da mace ke yi, na ba ta damar zaben namijin da take so ya zama uban ‘ya’yanta. 

DARWIN: Ya ci gaba da cewa: “Ba siffa ce ta dami mace ba, amma mai iya kula da ita da biya mata bukata shi ne a gabanta. Babban abin farin ciki gare ta shi ne ta zama abin sha’awa da kauna da ta sami haka sai ta saduda. 

LOMBROSO, KISCH, KRAFFT-EBING  na cewa: “Kowace irin mace, ta mutane ko ta dabbobi ko ta tsuntsaye ba ta damu da jima’i ba.”

FILOSAFIYA BEATRICE MARBEAU: Tana cewa a cikin littafin ta mai suna ‘Halayen uwa’ Mace na bukatar mijin ta fiye da kullum a lokacin da take da ciki. Daga lokacin da ta farga cewa tana da ciki, a wannan lokaci hankalinta zai fara dagule wa. Za ta fara jin warin jikinta, tun ba ma a ce dan fari ne ba. Da zarar ta fara jin motsi, sai ta koma jin karar abin da ke ciki. Hakan zai kai ta ga tunani da canza halaye. Daga baya sai jin wani a cikin ta ya fara faranta mata rai, sai ta kai ga mancewa da komai, ta mai da hankali ga tunanin cikin kawai. A lokacin ta fi son a fahimce ta, a kuma kaunace ta. A taimaka mata, saboda komai kyawunta a lokacin zai ragu. Ga ciwo daban-daban da zai iya damunta. A karshe ga tsoron haihuwa. 

Exit mobile version