Fakewa Da Batun Kasar Sin Ba Zai Taimaka Wa NATO Cimma Burinta Da Ya Shafi Yankin Asiya Da Tekun Pasifik Ba
  • English
  • Business News
Wednesday, October 8, 2025
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Fakewa Da Batun Kasar Sin Ba Zai Taimaka Wa NATO Cimma Burinta Da Ya Shafi Yankin Asiya Da Tekun Pasifik Ba

bySulaiman and CGTN Hausa
1 year ago
Pasifik

Za a kaddamar da taron kolin kungiyar tsaro ta NATO a yau Talata 9 ga wata a birnin Washington dake kasar Amurka. A wajen taron manema labarai da aka shirya kafin taron, babban magatakardan kungiyar, Jens Stoltenberg ya ce, kungiyar na bukatar fadada hadin-gwiwa tare da aminanta dake yankin tekun Indiya da Pasifik, da zummar shawo kan kasar Sin da sauran wasu kasashe, alamarin da a cewar kafafen yada labarai da dama, yunkuri ne da NATO ta yi ta hanyar fakewa da batun kasar Sin, domin yin shisshigi cikin harkokin yankin Asiya da tekun Pasifik, da nuna fin karfin Amurka kan sauran kasashe.

A matsayinta na kungiyar da aka kafa bayan yakin cacar baka, kana kungiyar soja mafi girma a duniya, tun kafuwarta har zuwa yanzu, NATO ta zama hanyar da Amurka ke amfani da ita, domin yin fito-na-fito da kawo cikas gami da matsa lamba ga sauran kasashe. A karkashin umarnin Amurka din, sanarwar da aka fitar a wajen tarukan kolin NATO a yan shekarun nan, ta sha rura wutar rikicin dake cewa, wai kasar Sin na haifar da barazana ga duniya, a wani yunkuri na maida kasar abokiyar hamayya, da tilastawa kasashen yankin Asiya da tekun Pasifik su zabi wace za su bi.

Tarihi na tafiya yadda ya kamata. Duk wutar rikicin da NATO ta rura, ba za ta boye gaskiya ba, wato NATO din, kungiya ce da ta wuce yayi, kana, ita ce asalin haifar da barazana ga duk fadin duniya. Manufar NATO kan yankin Asiya da tekun Pasifik, shiri ne dake yunkurin kawo baraka da tada zaune-tsaye har da yake-yake, da nufin taimakawa Amurka nuna babakere a duniya, wadda ta saba wa tarihi, kuma ba za ta yi nasara ba. (Murtala Zhang)

ShareTweetSendShare

MASU ALAKA

Kasar Sin Ta Yi Kira Ga Kasashen Duniya Su Hada Hannu Wajen Raya Harkokin Mata
Daga Birnin Sin

Kasar Sin Ta Yi Kira Ga Kasashen Duniya Su Hada Hannu Wajen Raya Harkokin Mata

October 7, 2025
Wakilin Sin Ya Ba Da Shawarwari Uku Kan Yaki Da Ta’addanci
Daga Birnin Sin

Wakilin Sin Ya Ba Da Shawarwari Uku Kan Yaki Da Ta’addanci

October 7, 2025
Sauyin Yanayi: “Damfara” Ko Gudun Sauke Nauyi?
Daga Birnin Sin

Sauyin Yanayi: “Damfara” Ko Gudun Sauke Nauyi?

October 7, 2025
Next Post
Shugaban Jami’ar FUDMA Ya Zargi Wasu Ma’aikatan Jami’ar da Taimakawa Ƴan Bindiga

Shugaban Jami'ar FUDMA Ya Zargi Wasu Ma'aikatan Jami'ar da Taimakawa Ƴan Bindiga

LABARAI MASU NASABA

ABU Na Kashe Sama Da Naira Biliyan 4 Duk Shekara A Wutar Lantarki

ABU Na Kashe Sama Da Naira Biliyan 4 Duk Shekara A Wutar Lantarki

October 8, 2025
Gwamnati Ta Roƙi ASUU Ta Soke Shiga Tsunduma Yajin Aiki, Ta Yi Alƙawarin Biyan Buƙatunsu

Gwamnati Ta Roƙi ASUU Ta Soke Shiga Tsunduma Yajin Aiki, Ta Yi Alƙawarin Biyan Buƙatunsu

October 8, 2025
Boko Haram Ta Taɓa Ayyana Buhari A Matsayin Wanda Zai Yi Mata Sulhu Da Gwamnati – Dalung

Boko Haram Ta Taɓa Ayyana Buhari A Matsayin Wanda Zai Yi Mata Sulhu Da Gwamnati – Dalung

October 8, 2025
A Kama Wani Likitan Bogi A Neja

‘Yansanda Sun Kama Masu Laifi 153, Sun Ƙwato Miyagun Ƙwayoyi A Jihar Jigawa

October 8, 2025
An Fara Biyan Ma’aikata Sabon Mafi Ƙarancin Albashin N70,000 A Borno

‘Yansanda Da Mutanen Gari Sun Daƙile Harin Boko Haram A Borno

October 8, 2025
…ACF Ta Nesanta Kanta Da Goyon Bayan Akpabio

‘Yan Nijeriya Sama Da Miliyan 33 Ne Ke Fama Da Matsananciyar Yunwa – Akpabio

October 8, 2025
Kasar Sin Ta Yi Kira Ga Kasashen Duniya Su Hada Hannu Wajen Raya Harkokin Mata

Kasar Sin Ta Yi Kira Ga Kasashen Duniya Su Hada Hannu Wajen Raya Harkokin Mata

October 7, 2025
Wakilin Sin Ya Ba Da Shawarwari Uku Kan Yaki Da Ta’addanci

Wakilin Sin Ya Ba Da Shawarwari Uku Kan Yaki Da Ta’addanci

October 7, 2025
Cika Shekaru 25 Da Kafuwa: ACF Ta Jadadda Kudirinta Na Samun Hadin Kai Da Zaman Lafiya

Cika Shekaru 25 Da Kafuwa: ACF Ta Jadadda Kudirinta Na Samun Hadin Kai Da Zaman Lafiya

October 7, 2025
Sauyin Yanayi: “Damfara” Ko Gudun Sauke Nauyi?

Sauyin Yanayi: “Damfara” Ko Gudun Sauke Nauyi?

October 7, 2025

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

Exit mobile version