Falalar Goman Farko Na Watan Fahimtar Sayyidina Umar (RA) Da Sayyidina Aliyu (RA) Kan Ramakon Ramadan A Goman Zulhajji
  • English
  • Business News
Thursday, October 9, 2025
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Falalar Goman Farko Na Watan Fahimtar Sayyidina Umar (RA) Da Sayyidina Aliyu (RA) Kan Ramakon Ramadan A Goman Zulhajji

byAbubakar Sulaiman
1 year ago
Sayyidina Umar

Ibn Sirina ya kasance yana kin a ce an yi azumin kwana goma, sai dai a ce kwana tara saboda gudun kar jahili ya zaci za a hada har da ranar sallah a ayi azumin. Ana cewa azumin kwana tara, sai dai in aka rava wa goman, ana nufin tara ne ba goma ba. Ya tabbata a Hadisi Manzon Allah (SAW) yana ce wa azumin da ake yi “azumin kwana goma” kuma tara ake yi.

Mun gode Allah ilimi ya yi yawa a yanzu, fahimta ta karu, da kyar ne za a samu wani jahili ya dage a kan cewa azumin kwana goma ne za a yi tun da ya zo a Hadisi da wannan lafazin, maimakon kwana tara da ake nufi asali. Manzon Allah ya ce duk wanda ya yi azumi ranar sallah ya sava masa (SAW).

  • Ko Kun Taba Jin Labarin Dausayin Jinbianxi Na Birnin Zhangjiajie A Kasar Sin?
  • LEADERSHIP Ta Jinjina Wa Shehu Isma’ila Mai Diwani Kan Shafin Dausayin Musulunci

Da a ce Dan’adam zai yi bakance ga Allah, ya ce ya yi wa Allah alkawari zai azumci kwana goman farkon Zulhajji, kwana tara kawai zai yi azumin, cewa goman nan duk ba wani abu ba ne. Ka ga ya ambaci goma, amma a shari’a tara ake nufi. Kuma babu ramuwa a kansa babu kaffara. Domin abin da shari’a ba ta yarda da shi ba, to babu shi.

Manzon Allah (SAW) ya ce duk wani sharadi da ba ya daga cikin shari’a babu shi. Wannan kwana goma da ake fada al’ada ce kamar yadda ya zo a cikin lafazin Hadisi, amma dai tara ake nufi; ba a yin azumi ranar sallah. Yinin sallah lokaci ne na nishadi, da ciye-ciye, da shan abubuwa na dadi, da Zikirai kamar yadda Manzon Allah ya fada.

Wasu malamai sun ce idan mutum ya dauki azumin kaffara (wanda a ka’ida idan aka sha guda daya sauran sun zube sai an sako daga farko) kuma abin ya cimma Ramadan (ba tare da ya kammala ba) to ya ajiye azumin kaffara ya ci gaba da na Ramadan, idan an ga wata kuma ba zai ci gaba a ranar sallah ba (idil Fidir, karamar sallah), ya ajiye ya ci abinci, kashegari ya ci gaba sai ya kara guda daya a kan ragowar da suka rage masa, tun da shari’a ce ta dauke masa yin azumin ranar sallah. Wannan ita ce gangariyar magana.

Wasu kuma suka ce, a’a, ko dai mutum ya kirge lokacin da zai yi kaffarar har ya gama ba tare da Ramadan ya tarad da shi ba ko kuwa idan ya sha ruwa kaffarar nan ta ruguje sai ya sake wata. Amma dai maganar malaman da suka ce ya ci gaba da kaffara ta fi inganta. Idan kuma sallah babba ce (Idil Kabir) ba kwana daya ce da ita ba, kwana hudu ce, ranar Idi da ayyamut tashriki (kwanakin yanyana nama), domin idan mutum bai samu yin layya ba a ranar sallah idan ya samu hali zai iya yi kashegari, idan bai samu ba zai iya yi bayan kwana biyu da sallah har zuwa kwana ukun nan.

To a nan mutum zai ajiye azumin (na kaffara) ne kwana hudu, ranar sallar da kwana uku bayanta. Kamar yadda ya zo a cikin Hadisi, an so a raya dararen kwana goman nan na farkon Zulhajji iya karfin mutum. Annabi (SAW) ya ce akwai darare biyar da Allah Tabaraka wa Ta’ala ba ya juya addu’a a cikinsu. Su ne farkon daren Rajab, daren rabin watan Sha’aban, daren Juma’a, da kuma daren Idin karamar sallah da daren Idin babbar sallah.

Wadannan ba a juyar da addu’a a cikinsu. Sai dai kuma a lura da malamai suka ce mutum ya raya daren iya karfinsa, kar kuma ya yi abin da zai iya hana shi fita sallar idi da safe, barci ya kwashe shi ko ya kasa samun karfin da zai iya gaggaisawa da jama’a. Don haka ana so ya dan yi ibada gwargwadon yadda zai samu barci, don ya samu fita Idi da gaggaisawa da jama’a, wannan ya fi a kan ya kwana ibada har sallar Idin ta kuvuce masa.

Ai fita sallar Idin ta fi wannan raya daren. Shi ya sa da mutum ya raya dare da ibada sai goshin asuba barci ya dauke shi ya kasa yin sallar farilla; gwara ya yi barcinsa ya tashi ya samu sallar asuba. Shehu Ibrahim Inyass (RA) ya ce, mutum ya zama Tauraro idan zai iya, idan ba zai iya ba ya zama Wata, idan ba zai iya ba ya zama Rana. Shehu ya ce Tauraro yana iya fitowa tun magriba ba zai fadi ba sai bayan asuba. Idan mutum ba shi da aiki da safe; ya yi ibada cikin dare har ya yi sallar asuba rana ta fito bayan ya dan sha shayi; shikenan sai ya kwanta abin sa kafin azuhur. Amma idan mutum yana da kasuwanci ko makaranta, to ya za a yi ya yi hakan?

Shehu ya ce idan mutum ba zai iya zama Tauraro ba sai ya zama Wata. Wata bai tava fitowa tun farkon dare ya tsaya har karshen dare ba. Idan jinjirin wata ne da Magriba zai fito, zuwa shabiyun dare za ka neme shi ka

rasa. Idan ya dan tsufa kamar 15 ga wata, shi kuma ba zai fito ba sai dan cikin dare zuwa asuba ya tafi (rabi da rabi ne shi). Ma’ana a nan za ka iya yin barci kuma sai ka tashi ka yi ibada. Shehu ya ce idan ba za ka iya ba, ka zama Rana, duk ayoyi ne na Allah; mutum sai ya yi ibadarsa da rana, duk na Allah ne. Illa dai kawai dare ya fi natsuwa, babu mai damunka da surutu.

Wasu malamai sun ce me ya sa kare ba shi da albarka duk da yana haihuwa da yawa a-kai-akai, amma saniya take da albarka duk da a shekara sau daya take haihuwa, kuma kullum yanka ta ake amma duk garin da ka je sai ka ga garken shanu? Malamai suka ce akwai dalili, kare zai yi ta haushinsa da yawace-yawace cikin dare; asuba na yi sai ya kwanta, ya gama tsalle-tsallensa da koke-kokensa cikin dare duk bai kwanta ba sai lokacin da ake samun albarka. Ita kuwa saniya za ka gan ta kwance tana barci shane-shane amma da zarar asuba ta yi za ka ga ta tashi.

Don haka ‘yan’uwa a rinka kula kwarai da gaske, asuba din nan lokacin albarka ne. Hadisai sun zo a kan amsa addu’a a cikin daren Idi da kuma wadannan dararen na kwana goman farko na Zulhajji. Duk wanda ya yi addu’a a ciki; ba addu’ar yanke zumunta ba, Allah zai karva. Imamus Shafi’i ya so wadannan Hadisai ya ji dadinsu kwarai da gaske.

Fahimtar Sayyidina Umar (RA) Da Sayyidina Aliyu (RA) An yi savani na fahimta ko kuma na ra’ayi tsakanin Sayyadi Ali (Allah ya girmama fuskarsa) da Sayyidina Umar (RTA) cikin wadannan kwanaki 10 na Zulhajji. Sayyidina Umar ya ce: “wadannan kwanaki ga dai falalar su kowa ya ji da duk abin da Allah ya sanya a cikin su, to idan mutum yana da ramuwar azumunin Ramadana, ya rama a cikin wadannan kwanakin masu falala sai ya zamanto farilla a cikinsu kamr ta fifici farilla a Ramadanan ma.”

Wannan shi ne abin da Sayyidina Umar ya fada. Sayyidina Ali ya ce:” A’a, Kar a dauko wani aiki a kawo wa wadannan kwanaki goma masu albarka, a barsu da aikin su da Annabi ya fada musu. “In aka dauko Ramadana aka

kawo musu, sai a ce falalar ta Ramadana ce,” in ji sayyidina Ali. “Wadannan kwanaki sun fi kwanakin Ramadana, duk da girman Ramadana da abinda Allah ya zuba a cikin sa, ba wai Ramadana ba, wadannan kwanakin sun fi kwanakin Ramadana.

Kwanakin goman Zulhajji sun fi goman Karshen Ramadana. Sayyidina Ali ya cigaba da cewa, in aka debo wasu kwanaki na Ramadana aka ce za a zo a yi ramuwa a cikin wadannan kwanaki(goman Zulhajji) ce wa za a yi darajar ta wadancan ce (goman karshen Ramadana).

Don haka Sayyidina Ali ya ce ko ramuwar Ramadana ce a kanka kar ka yi su a wadannan kwanakin (goman Zulhajji). Wadannan kwanakin, an yi musu Nafila irin tasu ta kansu, in za ka iya, yi azumi kullumkullum da daddare yi ta Nafiloli, ko dai duk ibadar da ka ga za ka iya, ko karatun Al’kur’ani ko yabon Manzon Allah, ko kuma yi ta Zikiri iya karfinka.” Wannan ita ce maganar Sayyidina Ali.

Mun gode Allah masu Darikoki muna da wuridinmu na safe ga na yamma ga wazifa. To bayan wadannan kwankin sun wuce, bayan Sallah to ka rama azuminka. Sayyidina Ali yana ganin Nafila a wannan kwanaki ta dara farillolin duk wasu kwanakin ma, to ya za a yi a kawo wasu aiki.

To irin wadannan magana ta a saita girman musulunci da girman Ilimi duk shi ya kawo wannan savanin. Wannan ba wai suka ba ce ko a ce jama’a za ta rarrabu, fahimta ce, shima Sayyidina Umar ba cewa ya yi kwanakin ba su da daraja ba, shi ya ga to ga wani aiki can mai daraja da aka bari to a dauka a kawo su cikin kwanaki masu daraja.

Malamai na cewa “idan rashin lafiya ce ta sa mutum ya sha azumin watan Ramadana, ko tafiya ko dai duk abin da karatu ya yarda a ajiye azumin, to yanzu kwanakin da yake ramawa azumin su ma Ramadana ne”

ShareTweetSendShare

MASU ALAKA

Annabi (SAW) Shi Ne Mai Girman Duk Wani Mai Girma Da Allah Ya Taba Yi
Dausayin Musulunci

Annabi (SAW) Shi Ne Mai Girman Duk Wani Mai Girma Da Allah Ya Taba Yi

October 3, 2025
Murnar Maulidin Cikar Manzon Allah (SAW) Shekara 1,500 Da Haihuwa (3)
Dausayin Musulunci

Murnar Maulidin Cikar Manzon Allah (SAW) Shekara 1,500 Da Haihuwa (3)

September 26, 2025
Manzon Allah
Dausayin Musulunci

Muna Murna Da Maulidin Cikar Manzon Allah (SAW) Shekara 1,500 Da Haihuwa (1)

September 5, 2025
Next Post
INEC Ta Yi Wa  Jam’iyyun  Siyasa Gori A  Kan Rajistar  Mambobi

INEC Ta Yi Wa Jam’iyyun Siyasa Gori A Kan Rajistar Mambobi

LABARAI MASU NASABA

Tawagar Likitocin Sin Dake Saliyo Ta Gudanar Da Tiyatar Dashen Yatsa Irinta Ta Farko

Tawagar Likitocin Sin Dake Saliyo Ta Gudanar Da Tiyatar Dashen Yatsa Irinta Ta Farko

October 8, 2025
Babban Yankin Sin Ya Soki Lamirin Kalaman Aware Na Jagoran Yankin Taiwan

Babban Yankin Sin Ya Soki Lamirin Kalaman Aware Na Jagoran Yankin Taiwan

October 8, 2025
Yawan Zirga-Zirgar Jiragen Kasa Tsakanin Sin Da Turai Kan Layin Dogo Na Tsakiya Ya Zarce 3,000 A Bana

Yawan Zirga-Zirgar Jiragen Kasa Tsakanin Sin Da Turai Kan Layin Dogo Na Tsakiya Ya Zarce 3,000 A Bana

October 8, 2025
Majalisa Ta Nemi Jami’an Tsaro Su Ceto Daliban Jami’ar Gusau 30 Da Aka Sace

Kafa ‘Yansandan Jihohi Na Da Matuƙar Muhimmanci Wajen Magance Matsalar Rashin Tsaro

October 8, 2025
Adadin Kudaden Da Gidajen Sinima Na Sin Suka Tara Yayin Hutun Bikin Ranar Kasa Ya Haura Yuan Biliyan 1.7

Adadin Kudaden Da Gidajen Sinima Na Sin Suka Tara Yayin Hutun Bikin Ranar Kasa Ya Haura Yuan Biliyan 1.7

October 8, 2025
Tinubu

Tinubu Na Son A Saka Hannun Jari Da Kuɗaɗen Fansho A Ɓangaren Mai Da Iskar Gas

October 8, 2025
Gwamnatin Nasarawa Za Ta Hukunta Duk Masu Amfani Da Sinadiran Kamun Kifi Acikin Ruwa

Gwamnatin Nasarawa Za Ta Hukunta Duk Masu Amfani Da Sinadiran Kamun Kifi Acikin Ruwa

October 8, 2025
Sin: Ana Sa Ran Jigilar Fasinjoji Fiye Da Miliyan 21 A Yau Ta Jiragen Kasa

Sin: Ana Sa Ran Jigilar Fasinjoji Fiye Da Miliyan 21 A Yau Ta Jiragen Kasa

October 8, 2025
Kwastam Ta Kama Lita 35,000 Na Man Fetur, Tabar Wiwi Da Sauran Kayayyaki A Kebbi

Kwastam Ta Kama Lita 35,000 Na Man Fetur, Tabar Wiwi Da Sauran Kayayyaki A Kebbi

October 8, 2025
Sin Ta Yi Kira Ga Mambobin WTO Da Su Tinkari Yanayin Tangal-Tangal Tare

Sin Ta Yi Kira Ga Mambobin WTO Da Su Tinkari Yanayin Tangal-Tangal Tare

October 8, 2025

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

Exit mobile version