Falalar Goman Farko Na Watan Zulhajji (6): Bayanan Malamai Kan Tabbatar Da Azumtar Kwanakin (II)

Zulhajji

Masu karatu assalamu alaikum wa rahmtullah. Kafin mu shiga sabon karatu na yau za mu dan yi waiwaye kadan a kan darasin makon da ya wuce domin a fahimci darasin namu na yau kamar yadda ya kamata

Ibn Sirina ya kasance yana kin a ce an yi azumin kwana goma, sai dai a ce kwana tara saboda gudun kar jahili ya zaci za a hada har da ranar sallah a ayi azumin. Ana cewa azumin kwana tara, sai dai in aka raba wa goman, ana nufin tara ne ba goma ba. Ya tabbata a Hadisi Manzon Allah (SAW) yana ce wa azumin da ake yi “azumin kwana goma” kuma tara ake yi. Mun gode Allah ilimi ya yi yawa a yanzu, fahimta ta karu, da kyar ne za a samu wani jahili ya dage a kan cewa azumin kwana goma ne za a yi tun da ya zo a Hadisi da wannan lafazin, maimakon kwana tara da ake nufi asali. Manzon Allah ya ce duk wanda ya yi azumi ranar sallah ya saba masa (SAW).

Da a ce Dan Adam zai yi bakance ga Allah, ya ce ya yi wa Allah alkawari zai azumci kwana goman farkon Zulhajji, kwana tara kawai zai yi azumin, cewa goman nan duk ba wani abu ba ne. Ka ga ya ambaci goma, amma a shari’a tara ake nufi. Kuma babu ramuwa a kansa babu kaffara. Domin abin da shari’a ba ta yarda da shi ba, to babu shi. Manzon Allah (SAW) ya ce duk wani sharadi da ba ya daga cikin shari’a babu shi. Wannan kwana goma da ake fada al’ada ce kamar yadda ya zo a cikin lafazin Hadisi, amma dai tara ake nufi; ba azumi ranar sallah. Yinin sallah lokaci ne na nishadi, da ciye-ciye, da shan abubuwa na dadi, da Zikirai kamar yadda Manzon Allah ya fada.

Wasu malamai sun ce idan mutum ya dauki azumin kaffara (wanda a ka’ida idan aka sha guda daya sauran sun zube sai an sako daga farko) kuma abin ya cimma Ramadan (ba tare da ya kammala ba) to ya ajiye azumin kaffara ya ci gaba da na Ramadan, idan an ga wata kuma ba zai ci gaba a ranar sallah ba (dil Fidir, karamar sallah), ya ajiye ya ci abinci, kashegari ya ci gaba sai ya kara guda daya a kan ragowar da suka rage masa, tun da shari’a ce ta dauke masa yin azumin ranar sallah. Wannan ita ce gangariyar magana. Wasu kuma suka ce, a’a, ko dai mutum ya kirge lokacin da zai yi kaffarar har ya gama ba tare da Ramadan ya tarad da shi ba ko kuwa idan ya sha ruwa kaffarar nan ta ruguje sai ya sake wata. Amma dai maganar malaman da suka ce ya ci gaba da kaffara ta fi inganta. Idan kuma sallah babba ce (Idil Kabir) ba kwana daya ce da ita ba, kwana hudu ce, ranar Idi da ayyamut tashriki (kwanakin yanyana nama), domin idan mutum bai samu yin layya ba a ranar sallah idan ya samu hali zai iya yi kashegari, idan bai samu ba zai iya yi bayan kwana biyu da sallah har zuwa kwana ukun nan. To a nan mutum zai ajiye azumin (na kaffara) ne kwana hudu, ranar sallar da kwana uku bayanta.

Kamar yadda ya zo a cikin Hadisi, an so a raya dararen kwana goman nan na farkon Zulhajji iya karfin mutum. Annabi (SAW) ya ce akwai darare biyar da Allah Tabaraka wa Ta’ala ba ya juya addu’a a cikinsu. Su ne farkon daren Rajab, daren rabin watan Sha’aban, daren Juma’a, da kuma daren Idin karamar sallah da daren Idin babbar sallah. Wadannan ba a juyar da addu’a a cikinsu. Sai dai kuma a lura da malamai suka ce mutum ya raya daren iya karfinsa, kar kuma ya yi abin da zai iya hana shi fita sallar idi da safe, barci ya kwashe shi ko ya kasa samun karfin da zai iya gaggaisawa da jama’a. Don haka ana so ya dan yi ibada gwargwadon yadda zai samu barci, don ya samu fita Idi da gaggaisawa da jama’a, wannan ya fi a kan ya kwana ibada har sallar Idin ta kubuce masa. Ai fita sallar Idin ta fi wannan raya daren. Shi ya sa da mutum ya raya dare da ibada sai goshin asuba barci ya dauke shi ya kasa yin sallar farilla; gwara ya yi barcinsa ya tashi ya samu sallar asuba. Shehu Ibrahim (RA) ya ce, mutum ya zama Tauraro idan zai iya, idan ba zai iya ba ya zama Wata, idan ba zai iya ba ya zama Rana. Shehu ya ce Tauraro yana iya fitowa tun magriba ba zai fadi ba sai bayan asuba. Idan mutum ba shi da aiki da safe; ya yi ibada cikin dare har ya yi sallar asuba rana ta fito bayan ya dan sha shayi; shikenan sai ya kwanta abin sa kafin azuhur. Amma idan mutum yana da kasuwanci ko makaranta, to ya za a yi ya yi hakan? Shehu ya ce idan mutum ba zai iya zama Tauraro ba sai ya zama Wata. Wata bai taba fitowa tun farkon dare ya tsaya har karshen dare ba. Idan jinjirin wata ne da Magriba zai fito, zuwa shabiyun dare za ka neme shi ka rasa. Idan ya dan tsufa kamar 15 ga wata, shi kuma ba zai fito ba sai dan cikin dare zuwa asuba ya tafi (rabi da rabi ne shi).

Ma’ana a nan za ka iya yin barci kuma sai ka tashi ka yi ibada. Shehu ya ce idan ba za ka iya ba, ka zama Rana, duk ayoyi ne na Allah; mutum sai ya yi ibadarsa da rana, duk na Allah ne. Illa dai kawai dare ya fi natsuwa, babu mai damunka da surutu. Wasu malamai sun ce me ya sa kare ba shi da albarka duk da yana haihuwa da yawa a-kai-a-kai, amma saniya take da albarka duk da a shekara sau daya take haihuwa, kuma kullum yanka ta ake amma duk garin da ka je sai ka ga garken shanu? Malamai suka ce akwai dalili, kare zai yi ta haushinsa da yawace-yawace cikin dare; asuba na yi sai ya kwanta, ya gama tsalle-tsallensa da koke-kokensa cikin dare duk bai kwanta ba sai lokacin da ake samun albarka. Ita kuwa saniya za ka gan ta kwance tana barci shane-shane amma da zarar asuba ta yi za ka ga ta tashi. Don haka ‘yan’uwa a rinka kula kwarai da gaske, asuba din nan lokacin albarka ne.

Hadisai sun zo a kan amsa addu’a a cikin daren Idi da kuma wadannan dararen na kwana goman farko na Zulhajji. Duk wanda ya yi addu’a a ciki; ba addu’ar yanke zumunta ba, Allah zai karba. Imamus Shafi’i ya so wadannan Hadisai ya ji dadinsu kwarai da gaske.

 

 

Exit mobile version