Leadership Hausa Newspapers
No Result
View All Result
  • LABARAI
  • WASANNI
  • RAHOTANNI
  • SIYASA
  • KASUWANCI
  • ADABI
  • RA’AYINMU
  • TATTAUNAWA
  • BIDIYO
  • MAKALAR YAU
  • LABARAI
  • WASANNI
  • RAHOTANNI
  • SIYASA
  • KASUWANCI
  • ADABI
  • RA’AYINMU
  • TATTAUNAWA
  • BIDIYO
  • MAKALAR YAU
No Result
View All Result
Leadership Hausa Newspapers
No Result
View All Result
Home DAUSAYIN MUSULUNCI

Falalar Ziyarar Kabarin Annabi SAW (1)

by Tayo Adelaja
September 2, 2017
in DAUSAYIN MUSULUNCI
5 min read
WhatsAppShare on FacebookShare on TwitterShare on Telegram

Tare da Sayyid Isma’il Umar (Mai Diwani)

Ziyarar kabarin Manzon Allah (SAW) tana daga cikin ibadu mafi girma da samun kusanci zuwa ga Allah (SWT). Babu wata ibada da ta kai darajar Manzon Allah (SAW) a wurin Allah. Babu wani abu da Musulmi zai yi Allah ya ji dadi (yadda ya dace da shi SWT) kamar girmama Masoyinsa Manzon Allah (SAW). Domin girmama Manzon Allah, girmama Allah ne da ya aiko shi. Kuma ziyararsa (SAW), tana daga cikin girmama shi.

samndaads

An karbo Hadisi daga Ummul-Mu’umina Aisha (RA) cewa Manzon Allah (SAW) ya ce, “Ni ne cikamakon Annabawa, Masallacina ne cikamakon Masallatan Annabawa, shi ne mafi cancantar Masallacin da za a daura kaya musamman don ziyartarsa.”

A nan, ba ana nufin cewa a ziyarci Masallacin ne muradi ba kawai, domin ai Masallacin ya daran ma sauran Masallatau ne saboda kasancewarsa na Manzon Allah (SAW).

Dukkan darajoji da martabobin da Allah ya baiwa Annabawa, ya tara wa Annabi (SAW) kuma ya kara ma sa da wasu na daban.

Idan aka dubi wannan, bai kamata a rika bata karatu ana cewa Masallaci ne za a ziyarta amma ba Annabi (SAW) ba. Ya kamata a gyara karatu, a gyara wannan fahimtar. Saboda irin wannan fahimtar ce ta haifar da a zamanin nan an samu rashin girmama Manzon Allah (SAW) har aka dasa bom kusa da shi a shekarar bara. Ko daga murya Allah ya hana a yi a gaban Annabi (SAW), to ina ga tada bom?

Duk ire-iren karatuttukan nan ne na rashin ganin girman Annabi (SAW) suke jawo wadannan bala’o’in. Ya kamata a ji tsoron Allah a gyara.

Malamai Malikawa sun yi hukuncin cewa zuwa ziyara a Madina wajibi ne ga wanda yake da hali. Ma’ana idan mutum ya yi Aikin Hajji, wajibi ne ya ziyarci Manzon Allah (SAW) idan yana da halin zuwa.

Masu cewa idan mutum ya yi Hajji shikenan ba sai ya tafi ziyarar ba, suna nuna alama ce ta kin Manzon Allah (SAW).

Hadisai masu yawa sun yi bayani a kan falalar ziyarar Manzon Allah (SAW).

Yana daga ciki, Abdullahi bin Umar (RA) ya ruwaito cewa, Manzon Allah (SAW) ya ce, “Duk wanda ya yi Hajji, sai ya ziyarci kabarina bayan mutuwata, ya zama kamar wanda ya ziyarce ni ne lokacin da nake da rai.” Ma’ana duk daya suke.

Dukkanin malamai na Allah Ahlus Sunnah tun daga kan Sahabbai a kan wannan fahimtar suke.

Haka nan, Hadisi ya tabbata daga Abdullahi bin Umar (RA) cewa, Manzon Allah (SAW) ya ce, “Duk wanda ya ziyarci kabarina, cetona ya cancanta a gare shi”. Abu Haraira (RA) ya ruwaito Hadisi daga Manzon Allah (SAW) ya ce, “Babu wani mutum da zai yi sallama a gare ni, face Allah ya dawo mun da raina har na amsa sallamar.”

Idan mutum zai je ziyarar, walau Alhaji ko wanda ba Alhaji ba, zai yi niyyar cewa zai je ya ziyarci Manzon Allah (SAW), sannan ya yi sallah a Masallacinsa, ya ziyarci sauran Sahabbai da wuraren Musulunci. Amma dai Annabi (SAW) ne a kan gaba.

Ana so idan mai ziyara ya tasam ma Madinar Annabi (SAW), ya yawaita salati ga Manzon Allah (SAW) domin ya kara samun haske da soyayyarsa (SAW).

Haka nan, ana so mutum ya yi wanka, ya sa turare, ya sa tufafinsa mafi kyau, kuma ya jaddada tubansa, sannan ya halarto da girman Annabi (SAW) a cikin zuciyarsa, da girman Sahabbansa, da ganin girman garin baki daya (a matsayin wurin da Annabi (SAW) da Iyalansa da Sahabbansa suka rayu, da faruwar abubuwan tarihi na Musulunci. Lallai idan mutum ya yi haka, zai ji wani karin imani har ya sa shi kuka.

Idan mai ziyara ya zo shiga Masallacin Annabi (SAW), ana so ya shiga da kafar dama ya ce “A’uzubillahil azim wa bi wajhihil karim wa suldanihil kadim minas shaidanir rajim, bismillah, allahumma salli ala Muhammadin wa alihi wa sallim, allahummagfirli zunubi waftahali abwaba rahmatika.”

Idan da hali ya yi kokari ya shiga Raula (wurin da Annabi ya ce Dausayin Aljanna ne) ya yi sallah nafila raka’a biyu a matsayin gaisuwar Masallaci. Idan kuma Raula ta cika, sai a yi sallar a duk wurin da aka samu a Masallacin.

Daga nan, idan lokacin ya kasance lokacin sallar farilla ne sai ya tsaya a kammala sallar, idan kuma ba lokacinta ne ba, yana idar da nafilar sai ya nufi ziyarar Annabi (SAW).

Idan ya zo wurin kabarin mai girma, sai ya baiwa alkibla baya; ya fuskanci bangon kabarin kusa da inda hukuma ta amince a tsaya. Ya halarto da girman Annabi (SAW) tare da tunanin cewa ga fuskar Annabi (SAW) tana kallonsa. Sai ya yi sallama cikin ladabi na sarari da boye, sannan ya yi salati ga Manzon Allah (SAW). Ma’ana ya ce”Assalamu alaika ya Rasulullah, assalamu alaika ya Nabiyyallah, assalamu alaika ya Khaira khalkillah, assallamu alaika ya Habiballah, assalamu alaika ya Sayyidal Murasalin, assalamu alaika ya rasula Rabbul alamin, assalamu alaika ya ka’ida gurril muhajjalin. Ash’hadu an la’ilaha illallah wa ash’hadu annaka abduhu wa rasuluhu wa aminuhu wa khiratuhu Wa ash’hadu annaka kad ballagtar risalata wa addaital amanata wa nasahtal ummata wa jahada fillahi hakka jihadihi.”

Sai mutum ya karanta ayar nan ta neman gafarar Allah a wurinsa (SAW) ta cikin Suratun Nisa’i. Idan ya samu hali sai ya dan ja baya kadan ya yi salati guda 70 ga Annabi (SAW).

Daga nan ya matsa daidai kamu daya a dama, ya yi sallama ga Sayyidina Abubakar (RA), kuma ya kara matsawa irin haka duk dai a dama, ya yi sallama ga Sayyidina Umar (RA). Daga nan sai ya fice ya kammala ziyara.

Haka Malaman da ke da soyayyar Manzon Allah (SAW) a zuciyarsu suka fahimci Hadisin.

……..

SendShareTweetShare
Previous Post

Garabasa Da Falalar Ranar Arfa

Next Post

Falalar Ziyarar Kabarin Annabi SAW (2)

RelatedPosts

Darajojin

Darajojin Manzon Allah (SAW) Da Suratul Fat’hi Ta Tattare (II)

by Muhammad
1 day ago
0

Allah ya ce wa Manzon Allah (SAW) “Mu muka aiko...

kebance

Kebance-kebancen Manzon Allah (SAW) II

by Muhammad
2 weeks ago
0

Daga Sayyadi Ismail Umar Mai Diwani, Masu karatu assalamu alaikum...

Kebance-kebancen Manzon Allah

Kebance-kebancen Manzon Allah (SAW) I

by Sulaiman Ibrahim
3 weeks ago
0

A uzu billahi minas shaidanin rajim. Bismillahir rahmanir Rahim. Wa...

Next Post

Falalar Ziyarar Kabarin Annabi SAW (2)

Leave a Reply Cancel reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Domin sanya talla ko karin bayani a tuntube wannan numbar +2348126152609.

Leadership Epaper
ADVERTISEMENT
  • LABARAI
  • WASANNI
  • RAHOTANNI
  • SIYASA
  • KASUWANCI
  • ADABI
  • RA’AYINMU
  • TATTAUNAWA
  • BIDIYO
  • MAKALAR YAU
Advertise with us

© 2020 Leadership Group .

No Result
View All Result
  • LABARAI
  • WASANNI
  • RAHOTANNI
  • SIYASA
  • KASUWANCI
  • ADABI
  • RA’AYINMU
  • TATTAUNAWA
  • BIDIYO
  • MAKALAR YAU

© 2020 Leadership Group .

Go to mobile version