Abubakar Abba" />

Fannin Aikin Noma A Nijeriya Na Fuskantar Kalubale, Cewar Manaja

Kalubalen da ke a cikin fannin aikin noma a Nijeriya suna da yawan gaske ya kuma zama wajibi gwamnatin tarayya ta dauki matakan magance su.

Bayanin hakan ya fito ne daga bakin Manajin Darakata na rukunonin Kamfanin Wal-Wanne Dakta Abiso Kabir, inda Manajin Darakata na rukunonin Kamfanin Wal-wanne Dakta Abiso Kabir ya yi nuni da cewa, ya zama wajibi gwamnati ta samar da tsare-tsaren da zasu inganta fitar da amfanin gona da aka noma a kasar nan zuwa kasuwannin duniya.

Ya sanar da hakan ne a cikin wata sanarwa da ya fitar a jihar Legas, inda Dakta Kabir yaci gaba da cewa, kalubalen dake a cikin fannin aikin noma suna da yawan gaske, harda gazawar samarwa da manoman kasar nan samun damar fitar da amfanin su da suka noma zuwa kasuwannin kasashen ketare.

A cewar Manajin Darakata na rukunonin Kamfanin Wal-wanne Dakta Abiso Kabir, har ila yau gazawar manoman kasar nan wajen cika sharuddan bukatun kasa da kasa na fitar da amfanin gona zuwa kasashen waje da suka shafi lafiyar amfanin gonakan su, yana daya daga cikin manyan kalubalen da ake fuskanta wajen yin kasuwanci tsakanin Nijeriya fa da sauran kasashen ketare.

Manajin Darakata na rukunonin Kamfanin Wal-wanne Dakta Abiso Kabir yaci gaba da cewa, butar da ake da ita ga ko wannen dan Nijeriya ya rungumii fannin noma, ya kasance daya daga cikin. Tsarin Gwamnatin Tarayya na ERGP da akayi shi a bisa farfado da tattalin arzikin Nijeriya.

A cewar Manajin Darakata na rukunonin Kamfanin Wal-wanne Dakta Abiso Kabir, Kamfanin na Wal-wanne ya kware wajen yin noma da kayan aiki na zamani, adana amfanin gona, da kuma yadda za’a rabar da amfanin gona da aka noma a kasar nan kuma kamfanin yana yin kokari kan samar da ayyuakn yi ta hanyar noma ga alumomi da dama dake Nijeriya.

Da ya ke yin tsikaci kan nasarorin Kamfanin Manajin Darakata na rukunonin Kamfanin Wal-wanne Dakta Abiso Kabir yace, Kamfanin na sarrafa Shinkafa Wal-wanne yana sarrafa Shinkafa tan-tan 120 a kulkum.

Ya cigaba da cewa, Kamfanin ya samunasarar samar da ayyukan yi, musamman a tsakanin mata da matasa, inda Manajin Darakata na rukunonin Kamfanin Wal-wanne Dakta Abiso Kabir ya sanar da cewa, Kamfanin ya tanadi tsare-tsare na bunkasa fannin noman Shinkfa ta hanyar yin amfani da kayan noma na zamani.

A cewar Manajin Darakata na rukunonin Kamfanin Wal-wanne Dakta Abiso Kabir, ta hanya samar da wadannan dabarun yin noma da kaayan aikin nowma na zamani, mun samu sukunin kara bunkasa fannin noma a kasar nan, inda wasu amfanin gonar za’a iya fitar dasu zuwa kasuwannin kasashen waje don siyarwa idan akayi la’akari da dimbin bukatar da ake dasu a kasar waje.

A karshe, Manajin Darakata na rukunonin Kamfanin Wal-wanne Dakta Abiso Kabir, zamuci gaba da samar da ayyukan yi ta hanyar fannin noma, musamman a tsakanin matasan dake kasar nan yadda suma zasu zamo masu dogaro da kansu.

Exit mobile version