Abubakar Abba" />

Fannin Noma Ne Mafita Wajen Bunkasa Arziki Fiye Da Fetur – Gwamna Umahi

Gwamna David Umahi na jihar Ebonyi ya yi kira ga alumnar jihar, musamman matasa su ka da su rungumi fannin aikin noma, gabin cewar, haryanzu fannin shi ne mafita wajen bunkasa tattalin arzikin kasa fiye da man fetur.

Gwamna Dabid Umahi wanda ya bayyana hakan yayin bikin kaddamar da sabbin shugabannin kungiyar masu samar da ingantaccen Irin noma ta kasa reshen jihar (NSSAN) a Cibiyar Taron Kasa da Kasa ta Akanu Ibiam, Abakaliki, ya yi nuni da cewa, ta hanyar rungumar noma, tattalin arzikin kasar zai iya bunkasa matuka.

Gwamna David Umahi wanda Kwamishinan ma’aikatar noma na jihar, Cif Musa Nomeh ya wakilce shi a wurin taron ya kara da cewa yayin da matasa ke shiga harkar Noma, za a rage yawan matasa da ke zaune basa aikin yi.

A cewar Gwamna David Umahi,”Mu na da damar da yawa na albarkatun noma, inda ya ce, abinda da mu ke bukata yanzu shi ne tattalin arzikin da ke tafiyar da noma kamar yadda farashin mai ke tafiya kasa.”

Gwamna Dabid Umahi ya bayyana cewa, kasancewar matasa a cikin noma za su bunkasa tattalin arzikin kasa da rage munanan dabi’u, inda ya kara da cewa, za samar da yanayi mai kyau ga manoman.

A cewar A cewar Gwamna Dabid Umahi, mu na da dama da yawa a cikin noma, mu na taimaka wa matasa da su shiga harkar noma saboda akwai dama da yawa a ciki, inda ya ce, noma shi ne tabbataccen mu, madadin mai, inda Gwamna Dabid Umahi ya wara da cewa, Mun kawo kowane bayani game da noma a yankin.

A nasa jawabin, Shugaban kungiyar (NSSAN), Alhaji Sheriff Balogun ya bayyana cewa jihar “ita ce jiha ta farko a duk sassan Kudancin kasar nan da ta samu nasarar samar da wadataccen abinci.

Ya dace da mahimmanci bayyana a wannan Irin a yanzu shi ne wanda ke kan gaba wajen samun kudin shiga na ketare zuwa tattalin arzikin kasar a yau, inda ya kara da cewa, don haka, shawarar da manoma jihar Ebonyi su ka yanke na zabar Irin a gaba da sauran jihohin da ke Kudancin kasar, su ma da fatan za su amfana.

A wata sabuwa kuwa, Ortom ya sanar da cewa, gwamnatinsa zata yi dukkan mai yuwa wajen tabbatar da shirin yaci nasara a jihar ta Biniwe, inda Gwamnan ya sanar da hakan ne wani taron zuba jari a fannin noman kasuwanci da a ka gudanar a garin Makurdi.

Shirin na FTF wanda gwamnatin kasar Amurka ce ta samar dashi, shi ne ya shirya taron kuma gwamnatin ta kirkiro da ahirinnne don yaki da yunwa a daukacin fadin duniya da kuma samar da wadataccen abinci.

Gwamnan ya ci gaba da cewa, a bisa samun nasarar da shirin ya yi ne a jihar ta Biniwe, hakan a sanya gwamnatin jihar ta kafa ofishin shirin a jihar ta Biniwe.

Ya kuma jaddada cewa, zai yi dukkan abinda ya dace wajen tanin an bai wa manoman na kasuwanci dukkan horon da ya dace don su samu amfanin gona mai dimbin yawa.

A nasa jawabin tunda farko a wurin taron, Ma’aikatar noma da albarkantu na jihar Dakata Timothy Ijir, ya shawarci manoman a fannin na noman kasuwanci da ke a jihar ta Biniwe dasu rungumi shirin, musamman don su habaka fannin noman su na kasuwanci da kuma inganta ruwarsu.

Kwamishinan ya ci gaba da cewa, inda kwamishinan yankara da cewa, manoman za su amfana sosai in har sun rungumi shirin.

Kwamishinan ya yi nuni da cewa, hakan kuma zai ba su damar yin noma mai yawan gaske za su kuma dai yin noman gargajiya zuwa komawa na zamani, musamman ganin cewar, mafi yawancin manoman jihar, sun dogar ne kacokam, wajen yin noma ta hanyar gargajiya, sababin rungumar noman na zamani.

Exit mobile version