CRI Hausa">

Fannin Sarrafa Mutum Mutunin Inji Na Sin Ya Karu Da Kaso 19.1 A 2020

Ma’aikatar masana’antu da fasahar sadarwa ta kasar Sin MIIT, ta ce a shekarar 2020 da ta gabata, fannin sarrafa mutum mutunin inji na Sin, ya fadada da kaso 19.1 bisa dari cikin shekara guda. Hakan a cewar ma’aikatar, na da nasaba da karuwar bukatun kasuwa, da saurin ci gaba da fannin kwaikwayon tunanin bil Adama ke samu.

A bara, hada hadar sarrafa mutum mutunin inji ta Sin, ta haura sama da yadda aka yi hasashe da kaso 6 bisa dari a shekara, kamar dai yadda alkaluman MIIT suka nuna. Har ila yau, kasuwar mutum mutunin injuna masu ayyukan ba da hidima ta bunkasa, inda kudaden hada hadar sashen suka kai kudin Sin yuan biliyan 10.31, kwatankwacin dalar Amurka biliyan 1.6, adadin da ya karu da kaso 31.3 a shekarar 2020.
Yanzu haka dai, Sin na kokarin daga matsayin masana’antun ta masu aiwatar da manyan ayyuka, ta hanyar amfani da fasahohin zamani na kirkire kirkire, a gabar da take fuskantar raguwar al’ummun dake ganiyar ayyukan karfi, da kuma tsadar kwadago.
A shekarar 2016, mahukuntan Sin sun fitar da wasu ka’idoji, wadanda suka tanaji dabarun ninka yawan mutum mutunin injuna na aiki a manyan masana’antu da rubi 3, ta yadda ya zuwa shekarar 2020, yawan wadanda ake kerawa a shekara guda za su kai 100,000. (Mai fassarawa: Saminu daga CRI Hausa)

Exit mobile version