Masu bincike a Birtaniya sun fara gudanar da wani babban gwaji domin auna wata sabuwar allurar rigakafin cutar mura da aka samar. Wannan allurer wasu na ganin an samar da ita a daidai lokacin da ya dace.
Masu sa-kai kimanin 500, kama daga ‘yan shekara 65 zuwa sama ne za a yi wa allurar ta gwaji. An haɗa wannan allurar rigakafi ce ta yadda za ta iya aiki don kashe nau’o’in cutar mura da dama.
Sabuwar allurar na karfafa garkuwar jikin dan’adam ta yadda za ta iya kai farmaki ga sinadaran ginan jiki da ke can cikin ƙwayoyin cutar ɓirus na mura.
Rigakafin kuma za ta ba wa jiki kariya tsawon shekaru.
Kuma masu bincike sun yi hasashen sake yunƙurowar murar da za ta shiga cikin jama’a don haka suka ga bukatar sake fasalin rigakafin ta kowacce shekara.
Ana fatan cewa sabuwar allurar rigakafin za ta kashe zafin cutar a tsakanin mutanen da aka yi wa rigakafi amma mura ta ci gaba da addabarsu.