Leadership Hausa Newspapers
No Result
View All Result
  • LABARAI
  • WASANNI
  • RAHOTANNI
  • SIYASA
  • KASUWANCI
  • ADABI
  • RA’AYINMU
  • TATTAUNAWA
  • BIDIYO
  • MAKALAR YAU
  • LABARAI
  • WASANNI
  • RAHOTANNI
  • SIYASA
  • KASUWANCI
  • ADABI
  • RA’AYINMU
  • TATTAUNAWA
  • BIDIYO
  • MAKALAR YAU
No Result
View All Result
Leadership Hausa Newspapers
No Result
View All Result
ADVERTISEMENT
Home LABARAI

An Fara Yunkurin Sasanta Kwankwaso Da Ganduje

by Tayo Adelaja
September 25, 2017
in LABARAI, MANYAN LABARAI
1 min read
WhatsAppShare on FacebookShare on TwitterShare on Telegram

Daga Na’ima Abubakar, Kano

Sakamakon rashin jituwar da ake gani tana kara tsananta tsakanin Gwamna Dakta Abdullahi Umar Ganduje da Ubangidansa a siyasance, Tsohon Gwamnan Kano kuma Sanatan Kano ta tsakiya a yanzu, Injiniyar Rabiu Musa Kwankwaso, yanzu haka wata kungiyar kiyaye hakkin dan Adam ta fara yunkurin sasanta aminan junan biyu, kungiyar ta samar da kwamitin da su ka dorawa alhakin sasanta jiga-jigan jam’iyyar ta APC a Kano.

Shugaban Kungiyar mai suna ‘Rigar ’Yanci’, Kwamared Mustapha Haruna Khalifa ya ce,  ba zai yiwu  manyan ‘yan siyasa irinsu Injiniya Rabiu Musa Kwankwaso da Gwamna mai ci a yanzu Dakta Abdullahi Umar Ganduje a Kano, su ci gaba da kawo rikice-rikice karshe har ta kai ga zubar da jini. Musamman ma bisa la’akari da kasancewar Kwankwaso da Ganduje jiga-jigai a siyasar Jihar Kano, saboda haka rashin daidaito a tsakanin  mutanen biyu babban kalubale ne ga al’ummar jihar da ma Jam’iyyar ta APC, musamman mata da kananan yara.

Wannan dalili yasa wannan kungiya ta kafa wani kwamiti  domin gayyato wadannan mutane biyu domin samun matsaya tare da dinke barakar dake neman kassara ci gaban da ake bukata a tsakaninsu, wannan yunkuri ci gaba ne babba hakan kuma zai samar da zaman lafiya a Jihar Kano.

SendShareTweetShare
Previous Post

Shugaban Hukumar JAMB Ya Kalubalanci Manyan Nijeriya

Next Post

BABBAN LABARI: ‘Yan Biyafara Ba ’Yan Ta’adda Ba Ne –Gwamnatin Amurka

RelatedPosts

Jam’iyyar APC Ta Raba Tallafin Kayan Azumi Na Sama Da Naira Biliyan Daya A Zamfara

by Daurawa Daurawa
3 hours ago
0

Daga Hussaini Yero, Gusau Jam’iyyar APC reshen Jihar Zamfara, karkashin...

Taho-mu-gama Kan Shugabancin PDP A Kano

Taho-mu-gama Kan Shugabancin PDP A Kano

by Sulaiman Ibrahim
7 hours ago
0

Daga Yusuf Shu’aibu   Abin Da Ya Sa Tambuwal Yake...

Kananan Hukumomin Jihar Kano

Yadda Za A Kawo Karshen Ta’addanci A Arewa Maso Yamma — Gwamna Ganduje

by Sulaiman Ibrahim
7 hours ago
0

Daga Mahdi M. Muhamad Gwamnan jihar Kano, Abdullahi Umar Ganduje...

Next Post

BABBAN LABARI: 'Yan Biyafara Ba ’Yan Ta’adda Ba Ne –Gwamnatin Amurka

Leave a Reply Cancel reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Domin sanya talla ko karin bayani a tuntube wannan numbar +2348126152609.

ADVERTISEMENT
  • LABARAI
  • WASANNI
  • RAHOTANNI
  • SIYASA
  • KASUWANCI
  • ADABI
  • RA’AYINMU
  • TATTAUNAWA
  • BIDIYO
  • MAKALAR YAU
Advertise with us

© 2020 Leadership Group .

No Result
View All Result
  • LABARAI
  • WASANNI
  • RAHOTANNI
  • SIYASA
  • KASUWANCI
  • ADABI
  • RA’AYINMU
  • TATTAUNAWA
  • BIDIYO
  • MAKALAR YAU

© 2020 Leadership Group .

Go to mobile version