Leadership Hausa Newspapers
No Result
View All Result
  • LABARAI
  • WASANNI
  • RAHOTANNI
  • SIYASA
  • KASUWANCI
  • ADABI
  • RA’AYINMU
  • TATTAUNAWA
  • BIDIYO
  • MAKALAR YAU
  • LABARAI
  • WASANNI
  • RAHOTANNI
  • SIYASA
  • KASUWANCI
  • ADABI
  • RA’AYINMU
  • TATTAUNAWA
  • BIDIYO
  • MAKALAR YAU
No Result
View All Result
Leadership Hausa Newspapers
No Result
View All Result
ADVERTISEMENT
Home KASASHEN WAJE

Faransa Ta Bukaci Chadi Ta Gudanar Da Zaben ‘Yan Majalisu

by Tayo Adelaja
September 13, 2017
in KASASHEN WAJE
1 min read
WhatsAppShare on FacebookShare on TwitterShare on Telegram

Kasar Faransa ta bukaci gwamnatin Chadi ta gudanar da zaben ’Yan Majalisu bayan kasashen duniya da ke bada agajin sun yi alkawarin taimaka mata da makudan kudade domin farfado da tattalin arzikinta da ke tangal tangal.

Kiran na Faransa ya biyo bayan ikrarin shugaba Idris Deby a watan Fabarairun wannan shekara cewar kasar bata da kudaden da za ta gudanar da zaben Yan Majalisu.

Mai Magana da yawun ma’aikatar harkokin wajen Faransa Agnes Romatet-Espagne ta shaidawa manema labarai cewar zaben ’Yan Majalisun na da matukar tasiri wajen tabbatar da dimokiradiya.

Ranar Juma’ar da ta gabata, gwamnatin Chadi ta ce, ta samu alkawarin tallafin da ya kai sama da Dala biliyan 18 domin bunkasa ci gaban kasar tsakanin shekarar 2017 zuwa 2021, wanda ya ribanya hasashen da ta yi.

Romatet-Espagne ta ce, daga cikin kudaden Faransa za ta bai wa Chadi euro miliyan 233.

Kasar Chadi ta fuskanci matsaloli da dama da suka hada da tashin hankali a Gabashi da Kudancin ta, yayin da fari da amaliya kuma suka addabe ta.

Chadi ta taka rawa sosai wajen kai daukin soji a Mali da Janhuriyar Afirka ta Tsakiya da kuma yaki da kungiyar boko haram.

SendShareTweetShare
Previous Post

Gwamnatin Tarayya Za Ta Yi Hadin Gwiwa Da Majalisar Dinkin Duniya

Next Post

Tsarin Mulkin Togo: ‘Yan Adawa Sun Jajirce

RelatedPosts

Mijin Sarauniya Elizabeth Ta Ingila Ya Mutu

Mijin Sarauniya Elizabeth Ta Ingila Ya Mutu

by Muhammad
5 days ago
0

Rahotanni daga Fadar Buckingham ta kasar Ingila sun tabbatar da...

Nijer

Matan Nijer Sun Dage Kan ‘Yancinsu Bayan Kotu Ta Sako Wasu Shugabanninsu

by Muhammad
4 weeks ago
0

Daga Rabiu Ali Indabawa, Hukumomi a jamhuriyar Nijer sun sako...

Magufuli

Muhimman Abubuwa Goma Game Da Tsohon Shugaban Tanzaniya John Magufuli

by Muhammad
4 weeks ago
0

Daga Rabiu Ali Indabawa, Al'ummar kasar Tanzania suna zaman makokin...

Next Post

Tsarin Mulkin Togo: ‘Yan Adawa Sun Jajirce

Leave a Reply Cancel reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Domin sanya talla ko karin bayani a tuntube wannan numbar +2348126152609.

ADVERTISEMENT
  • LABARAI
  • WASANNI
  • RAHOTANNI
  • SIYASA
  • KASUWANCI
  • ADABI
  • RA’AYINMU
  • TATTAUNAWA
  • BIDIYO
  • MAKALAR YAU
Advertise with us

© 2020 Leadership Group .

No Result
View All Result
  • LABARAI
  • WASANNI
  • RAHOTANNI
  • SIYASA
  • KASUWANCI
  • ADABI
  • RA’AYINMU
  • TATTAUNAWA
  • BIDIYO
  • MAKALAR YAU

© 2020 Leadership Group .

Go to mobile version