Faransa Ta Bukaci Chadi Ta Gudanar Da Zaben ‘Yan Majalisu

Kasar Faransa ta bukaci gwamnatin Chadi ta gudanar da zaben ’Yan Majalisu bayan kasashen duniya da ke bada agajin sun yi alkawarin taimaka mata da makudan kudade domin farfado da tattalin arzikinta da ke tangal tangal.

Kiran na Faransa ya biyo bayan ikrarin shugaba Idris Deby a watan Fabarairun wannan shekara cewar kasar bata da kudaden da za ta gudanar da zaben Yan Majalisu.

Mai Magana da yawun ma’aikatar harkokin wajen Faransa Agnes Romatet-Espagne ta shaidawa manema labarai cewar zaben ’Yan Majalisun na da matukar tasiri wajen tabbatar da dimokiradiya.

Ranar Juma’ar da ta gabata, gwamnatin Chadi ta ce, ta samu alkawarin tallafin da ya kai sama da Dala biliyan 18 domin bunkasa ci gaban kasar tsakanin shekarar 2017 zuwa 2021, wanda ya ribanya hasashen da ta yi.

Romatet-Espagne ta ce, daga cikin kudaden Faransa za ta bai wa Chadi euro miliyan 233.

Kasar Chadi ta fuskanci matsaloli da dama da suka hada da tashin hankali a Gabashi da Kudancin ta, yayin da fari da amaliya kuma suka addabe ta.

Chadi ta taka rawa sosai wajen kai daukin soji a Mali da Janhuriyar Afirka ta Tsakiya da kuma yaki da kungiyar boko haram.

Exit mobile version