Bisa gayyatar Shugaban Faransa Firaministan Iraki Haider Al Abadi zai kai wata ziyara Faransa ranar 5 ga watan gobe, Shugabanin biyu Emmanuel Macron da Al Habadi za su gana, domin tattance hanyoyin da suka dace wajen ganin an dakile duk wata barrazana da kan iya kawo cikas ga kokarin hukumomin Iraki na sake dawo da doka da oda a sasan kasar.
Kasar Iraki ta ba da umarnin dakatar da sauka da tashin jiragen sama a birnin Arbil na yankin Kurdawa, wanda ke a matsayin martani ga zaben raba gardamar balewa daga kasar da kurdawan suka kada. Hukumomin Bagadaza sun ce za su ci gaba da matsin lambar tabbatar da cewa Kurdawan su mika kai. Wannan mataki ya fito daga hukumomin Bagdaza na a matsayin barrazana ga tattalin arzikin yankin a cewar kakakin ministan sufuri na yankin Kurdawa Oumed Mohamas.