Faranta Wa Mutane Rai Shi Ne Babban Buri Na A Harkar ‘Comedy’ —Sadam Usman

Comedy

Editanmu Bello Hamza, ya tattauana da wani matashi mai tashe a harkar wasan barkwanci da aka fi sani da ‘Comedy’ matashin mai suna Sadam Usman, ya bayyana wa editanmu yadda ya tsinci kansa a fagen harkar wasan barkwanci, da kuma irin fatan day a ked a shi, ya uma ba matasa ‘yan uwansa shawarwari akan bukatar su rungumi sana’a su kuma guji harjar shaye shaye, ga dai yadda hirar ta mu ta kasance.

Da farko zamu so ka gabatar mana da kanka da kuma yadda ka tsinci kanka a harka wasan Comedy

Sunana Sadam Usman, sanadiyyan fara aikin ‘Comedy’ na shi ne wani ne ya yi min magana amma kafin nan ina yin rawa ne, kuma dai gaskiya sai na lura mutane da dama ba su so, suna sukana kuma hakan tun baya damuna har yazo yana damuna, da yake dama ina sana’ar aski, akwai wata rana wani mutum da alama an bata masa rai a wani wuri, to sai na yi abin da ya faranta mashi, har sai yake bani shawarar cewa ya lura ina da baiwa na ba mutane dariya ya kamata in fara ‘comedy’,. To da farko dai mun fara aikin fim da wani amma daga baya abin ya rushe sakamakon wani tafiya da jagoran wasan ya yi, daga nan ni kuma sai na fara na wa, mun fara da guda daya, daga baya muka cigaba ba saurarawa.

Ya sunan comedy da kuka fara da shi?

Sunan shi ‘Matan Gida’, da mutane suka gani kuma suka nuna abin ya yi musu kuma kawai sai nima abin ya shiga rai na, har takai mutane suna tambayar mu idan suka ga bamu saki sabo ba, Kuma har da manyan mutane, har da masu suka na da farko suka zo suna karar karfafa ni, har takai muka bude shafi a Youtube mutane suna shiga suna gani.

Zuwa yanzu yaya karbuwar aikin ku a wajen jama’ai?

Gaskiya Alhamdulillah, mutane suna Nishadan tuwa dashi, akwai wata mata a gidanmu ta bayyana cewa gaskiya tana jin dadin shi sosai, mutane da dama a suka aiko mani da sako na karfafa giwwa akan wannan aiki, haka kuma yana kara bani karfin gwiwar cewa lallai nida wannan harka, mutu ka raba.

Zuwa yanzu kuna da kamar ‘Followers’ nawa a Youtube?

Gaskiya a tashin farko muna da mutum hamsin  da suka fara bin mu amma yanzu lamarin ya ya karu sosai, hakan ya sa nima na saki jiki sosai, saboda nasan al’umma suna yin maraba da aikin da muke yi.

Wani alkairi ka samu a wannan harkan na comedy?

Gaskiya na sanu alkairi da yawa na farko na samu shawarwari da dama daga wajen manyan mutane wasu sun yi min alkawari kuma akwai wani da muka yi ma aiki ya dauka babban kudi ya bani, Kuma wannan kudin ya taimaka min sosai saboda da shi na siya wasu abubuwa a shagona, gaskiya na samu alkairi sosai, abin sai dai ince alhamdulillah.

Wasu kalubale ne ka fuskanta a wannan harka na comedy?

Dama a kowane irin aiki ana samun matsala, akwai wani misali, wata rana zamu yi aiki a wani gida muka nemi izini wajen matan gidan muka ce ta fada wa mijin ta da yake mijin ta yana tafiye tafiye ne ashe bata fada masa ba, muna cikin aiki sai gashi ya dawo kuma hakan gaskiya bai mai dadi ba har ya fadama mana wasu magana hakan haka, amma daga ba baya mun sami fahimtar juna.

Wani Kira kake da shi ga matasa ‘yan uwanka?

Gaskiya ita dama rayuwa sai godiyar Allah kana ma da sana’a ya ka kasance balantana ma baka da shi, gaskiya zaman matashi haka ba shida sana’a, akwai matsala sosai, Ni dai abin da na yadda da shi shi ne idan kana sana’a tsakanin ka da Allah komin kankan, to Allah ba zai barka ba.

Toh ga wadanda suke so su sadu da kai ko kungiyar ku ta wane hanya za su bi?

Mu muna layin sabuwar makarbarta ne a Hayin Dogo Samaru Zariya, idan mutum ya nemi Jeje Group insha Allah za a kawoka.

Mun gode

Nima na gode

Exit mobile version