Farashin dizil ya yi tashin gwauron zabi wanda lita daya ya kai naira 250, hakan ya yi matukar raunata harkokin kasuwanci sakamakon rashin samun wutar lantarki. Rahotanni ya nuna cewa, wasu gidajen mai a Jihar Legas sun kara farashin, inda suke sayar da kowacce lita daya suna sayar da shi naira 250, yayin da wasu suke sayar da litar a tsakanin naira 220 zuwa naira 245.
Gidajan man da ke kan hanyar Oshodi zuwa Apapa suna sayar da litar dizir lita daya a kan naira 250, yayin da ake sayar da kowacce dizil kan naira 248 a Ikeja, sannan ana sayar da litar dizil a kan naira 240.
A cikin rahoton farashin dizil na hukumar kadiddiga ta kasa ta bayyana cewa, farashin dizil ya karu da kashi 0.22 wato kan naira 224.86 ga kowacce litar a watan Junairun shekarar 2021 daga naira 224.37 na watan Disambar shekarar 2020.
Ta kara da cewa, jihohin da suka fi fuskantar hauhawar farashin dizil din sun hada da Jihar Adamawa wanda ake sayar sa shi kan naira 268.33 da Zamfara kan naira 262.78 da kuma Kebbi wanda ake sayar da shi kan naira 257.50.
“Jihohin da suka sami karancin farashin dizil sun hada da Osun wanda ake sayarwa naira 194.60 da Anambra kan 195.83 da kuma Inugu wanda ake sayarwa kan naira 198.24,” inji hukumar NBS.
Ana saka farashin dizil ne daga farashin danyan mai wanda aka samu kari sakamakon yadda gwamnatin tarayya ta canja yanayin tsarin saka farashin, inda ake kayyade shi da farashin danyan mai a kasuwan duniya. An samu karuwar farashin danyan mai a kasuwan duniya fiye da kashi 25 a wannan shekara, inda a baya farashin gangan danyan man a kasuwar duniya yake kan dala 51.22.
Sai dai kuma a ranar Talata an samu karuwar farashin wanda ya kai na dala 65.25. Ana yawan amfani da dizil a wuraren harkokin kasuwanci sakamakon karancin wutar lantarki a cikin kasar nan.
Shugaban kungiyar kananan kasuwanci a Nijeriya, Mista Femi Egbesola ya bayyana cewa, samun karuwar farashin dizil a kwanakin nan ya yi matukar raunata harkokin kasuwanci musamman ma kananan kasuwanci a cikin kasar nan.
“karuwar farashin dizil da na kayayyakin da muke sarrafawa yana matukar girgiza sha’anin kasuwancinmu. Marashin dizil ya jefa masu masana’antu cikin mawuyacin hali,” inji shi.
A cewarsa, yana yi wa harkokin kasuwanci hakasu wannan karin farashin dizil wajen saka farashi na kaarshe a kan kayayyaki.
Egbesola ya ce, “wannan ne ya sa mafi yawancin kamfanoni ke samar da kayayyaki da za su iya sayarwa a kasuwa a kadai, wanda suka daina samar da kayayyakin da sayar nan gaba, sai dai wanda suka tabbatar za su sayar a kasuwa.
“Mafi yawancin kamfanoni sun rage yawan kayayyakin da suke samarwa sakamakon tsadar dizil. Bai kamata a yi karin ba a dai-dai wannan lokaci, wanda hakan zai kara yawan marasa ayyukan yi. Yana kira da gwamnati ta yi wani abu a kan wannan lamari.”
Ya kara da cewa, tun da dai an gyara fannin bangaren mai, to ya kamata a yi kokarin dai-daita farashi ta yadda za a saukaka wa mutanen kasa. Egbesola ya ce, mafi yawancin kananan kasuwanci ba sa iya tanadar kudade, saboda muna amfani da kudadin da muka ijiye wajen ci gaba da gudanar da harkokin kasuwancinmu domin kar mu rufe shagunanmu.
Ya ce, “idan lamuran suka ci gaba da tafiya a haka, babu wata hanya dole sai mun rufe shagunanmu. Muna fama da karin da aka yi na wutar lantarki a kwanan na, sai kuma ga wani sabon karin farashin dizil.
“Mafi yawancin kananan kasuwanci sun dogara ne da dizil wajen saka wa janaretansu saboda babu isasshen wutar lantarki a cikin kasar nan. Manyan kamfanoni ne ke amfani da gas. Sannan ba za mu iya amfani da wutar lantarkin da ake samu daga hasken ran aba saboda ya yi tsada.”
Nijeriya ita ce tafi kowacce kasa a Afirka samar da mai, amma ta dogara ne da tace mai daga waje wanda ta kwashe shekaru da dama tana fama da wannan matsala.