Daga Abubakar Abba
Duk da saukar hauhawan farashi kayan abinci a ƙasar Najeriya, inda ya sauka da kashi 15.98 bisa ɗari saɓanin kamar yadda yake a 16.01 a baya, farashin kayan abincin sai ƙara tashin gwaron Zabo yake.
Hukumar Ƙididdiga ta Ƙasa (N BS) ce ta sanar da hakan a wani rahotonta na auna ma’aunin masu amfanin da abinci.
Hukumar ta bayyana hakan ne a cikin rahoton data fitar hauhawan farashin a watan Agusta kai 16.01 bisa ɗari, inda a watan Satumbar shekarar 2017 ya sauka zuwa 15.98 bisa ɗari.
Koda yake, farashin abinci sai ƙara tashi yake yi a ƙasar. Bugu da ƙari, rahoton kuma ya nuna cewar, hauhawan farshin kayan abinci daga 20.25 bisa ɗari, inda ya ƙaru zuwa 20.32 bisa ɗari a watan Agusta.
Ƙarin hauhawar farashin ya faru kamar akan, Dankali da Doya da Ƙwai da Burodi da Kofi da Nama da Kifi da Mai da sauransu, inda hauhawan farashin tafi ƙamari shi ne akan Suttura da kuɗin matafiya a cikin Jirgin Sama da Baburan hawa da Takalmi da kayan aras da kuma wasu kayayyakin gida.
Hauhawan farashin ya ƙara hawa zuwa 12. 30 bisa ɗari a watan Agusta, inda kuma ya ragu zuwa 12.10 bisa ɗari a watan Satumba.
Farashin Kayan abinci ya ƙaru da kashi 20.32 bisa ɗari a cikin shekara ɗaya, inda kuma a watan Satumba, farashin ya sauka zuwa kasha 0.07 bisa ɗari. Saɓanin yadda farashin ya hau zuwa kashi 20.25 bisa ɗari.