’Yan kasuwa a Nijeriya sun bayyana cewa, sakamakon yadda ake sayar da gangar danyen mai a kasuwar duniya a halin yanzu, farashin mai yana iya kai wa daga Naira 185 har zuwa Naira 200 a farashin kowacce litar man fetur, sai dai idan gwamnati da bayar da tallafi.
Sakamakon yadda gangar danyen mai ya kowa a kasuwan duniya ne ya sa ‘yan kasuwan yin wannan hasashe, kamar da ake kayyade farashin mai yadda kasuwan duna ta kama. Manyan kungiyoyin ‘yan kasuwan guda biyu sun bayyana wa manema labarai cewa, farashin mai zai ci gaba da karawa idan ba gwamnatin tarayya da dawo da zamanin bayar da tallafin mai ba.
Tun daga watan Disamba ce, ‘yan kasuwan suka dakon tsammanin sabon farashin man bisa karuwan farashin gangan mai da aka samu a kasuwan duniya, wanda ya kai dala 51.22 ga kowacce gangan mai a ranar 31 ga watan Disamba. Ganin yadda gwamnatin tarayya ta rage naira biyar a ranar 14 ga watan Disamba, ya sa ‘yan kasuwan suka fara shakkun kayyade farashin mai kamar yadda kasuwa ta kaya. Farashin danyan mai ne yake ci gaba da lakume kudade saboda yadda gwamnatin ke tace mai a kasashen ketare sannan a dawo da shi gida har a sayar.
A cewar ‘yan kasuwan, farashin litar mai zai iya kaiwa tsakanin naira 185 zuwa naira 200. A yanzu haka masu ana sayar da man ne a mafi yawancin gidajen mai da ke Legas kan naira 160 zuwa 165 ga kowacce litar mai.
“A yanzu haka ba za mu san yadda farashin zai kasance ba, amma muna has ashen farashin man zai iya kai wa a tsakanin naira 185 zuwa naira 200.
“Kamar yadda muke ci gaba da sayar da man a yanzu, babu wanda zai iya samun tallafi ko ma gwamnati ba za ta iya ci gaba da biya na a wannan lokaci,” in ji shi.
Ya kara da cewa, masu amfani da man fetur suna ta kara karuwa a cikin kasar nan a dai-dai lokacin da ake kara samun barazanar rarraba man. Isong ya ce, za a iya ci gaba da safarar man tun da dai farashin man ya sha bambam a tsakanin iyakokin kasar nan. Ya ce, da wannan ne muke kira ga gwamnatin tarayya ta yi kokarin sake gyara matatun mai ta yadda za a dunga tace mai a cikin gida Nijeriya wanda hakan zai kawo saukin farashin mai.
Kamfanin mai ta kasa (NNPC) shi ne kamfani guda daya da yake shigo da man daga kasashen wajen tun shekarun da suka gabata, duk da ‘yan kasuwa su suke rarraba mai a ko’ina a fadin kasar nan. kamfanonin ‘yan kasuwa sun dade suna sukar wannan lamari wanda suka bayyana cewa, akwai rashin dai-daituwar harkokin kasuwanci idan kamfanin NNPC ya ci gaba da shigo da man shi kadai.
Shi ma shugaban kungiyar ‘yan kasuwa masu rarraba man a Nijeriya, Mista Mike Osatuyi ya bayyana wa manema labarai cewa, ya kamata a kaddamar da sabon tsari wanda zai hana hauhawar farashin mai a cikin kasar nan.
Ya ce, “mun riga mun toshi hanyar bayar da tallafi, na tabbatar da haka ne daga bayanan da na samu, a duk kullum gwamnatin tarayya tana kashe naira biliyan 1.8, saboda lita miliyan 70 ake sayarwa a duk rana, sakamakon bude iyakokin kasar nan ne ya sa man yake zurarewa.
“A halin yanzu gwamnati ba ta iya biyan kudaden tallafi, sannan kuma babu kudaden tallafi a cikin kasafin kudi. Saboda haka, kasuwa iya take kayyade farashin man.
Osatuyi ya ci gaba da cewa, sakamakon kara farashin mai ya sa an samu hauhawar farashin dizil da kalanzir a cikin kasar nan.