Idris Umar" />

Farashin Naman Kare Na Kara Hauhawa A Zariya, Cewar Dadi

Exif_JPEG_420

Masu iya magana sun ce, abincin wani gubar wani. Wani matashi mai sana’ar fawa amma ta kare mai suna Dadi mazaunin anguwar Tabo dake samaru a karamar hukumar sabo Gari a jihar Kaduna ya tabbatar wa wakilinmu cewa yanzu naman kare ya yi tashin gwauran zabo a duk fadin kasuwannin naman kare dake zariya don haka duk wani mai mu’a’mula dashi saidai suyi hamuri karancin Marnukanne ya kawo hakan.

Dadi dan kimamin shekaru 30 ne a dukuniya acewarsa ya kai a kalla shekaru 11 yana sana’ar Fawa ta kare kuma da ita ya ke ci da sha harya taimaki iyayensa da wani abu.

Dadi ya ce abin da yake burgeshi a yanzu shine, yadda naman karen ke kara daraja a yanzu, kuma a lokaci guda masu cin naman karen suna kara ya wa ya ce a lokutan baya kabilu kadanne ke cin naman kare amma yanzu da sauran kabilun suka fahimci yadda Karen yake da dadi to yanzu rububin sa ake yi a duk fadin kasuwannin kare dake fadin kasannan.

To, ko tayaya mahautan karen ke samun galabar kare mai cizo idan ya zo mahautar ta kare, inda za a yanka shi? Dadi ya ce, yadda akewa samun kwararru wajan kayar da bijimin sa to haka muma muke da kwararru wajan zamge kare komin fadansa kuma komin girmansa .

To a ina ake suwo karen ga masu bukatar cinsa? Sai mahocin yace da yawan lokaci akan kawo wasu mahotar karnuka ne kuma yadda ake cika mota trela da shanu daga arewa zuwa kudancin Nigeriya haka muke cika mota trela da karnuka daga nan arewa zuwa kudancin Nigeriya.

Kuma a cewar mahocin karen a yanzu haka da kadan farashin kilon namansa ya zarta farashin naman kare a kasuwa nama.

Kuma hakan yasa ya an sani karin masu kiyon kare donci da masu kiwon kare da tsaro Wanda hakan yasa kasuwar kare ta kara daraja kuma sana’ar fawa ta Karen ta kara daukaka musamman a jihohin arewa da kudu baki daya.

Dadi yace, a yanzu kalubalen da sana’ar fawar kare ke fuskanta shine matsalar tsaro da ke fuskantar a kasa baki daya saboda a lokutan baya sukan yanka kare 10 zuwa 20 kuma su kare lokaci gida saboda manyan mutake na zuwa suna siyan naman amma yanzu bai wuce su yanka 5 ba saboda an sami canjin kasuwa manya mutanen najin tsoron zuwa siyan naman Karen don satar jama’a da ake fama dashi a halin yanzu da yin garguwa da ake fama dasu.

Kalubale na biyu shine yadda gwamnati take tallafawa kungiyar mahotan shanu da kudi don karfafa sana’ar fawa to su basa samun wannan tallafi don haka yayi kira ga gwamnati da su rika sanya mahotan kare a cikin tsari saboda muhimmancin su ga al’umma.

Bincike ya nuna cewa akan sami masu mu’a’mula da naman kare a kowace kabila mu samman a barukokin soja ko barkokin yan’sanda da akan kira Mami Maket. Kuma masu cin naman karen sun tabbatar da cewa naman kare yana da zaki fiye da naman akuya ko saniya bisa la’akkari da abicin da ya ke ci Kuma bincike ya nuna kare nada saurin yaduwa domin a shekara karya kan haifi yara 15 kuma bashi da wabi kamar sauran dabbobi. Kuma biciken ya nuna cewa masu kiwansa don tsaro sunfi masu kiwonsa don cinsa samun riba bisa dalili guda 1 na cewa zai wahala kaga wani yayi kiwon kare don ya yanka yaci kuma duk Karen da kaga an yankashi to ko bai da lafiya ko an satoshine don haka yasa masu kiwon sa don tsaro sunfi masu sana’ar cinsa riba.

Halittar kare wata halitta ce mai tattare da baiwa kalakala cikinsu akwai sabo da kaifin basira da rikon amana. Kare wasu kan kiwonsa don tsaron gida wasu kuma don kiwon dabbobi wasu kuma don binciken halittun dabbobi. Wasu suna cin namansa wasu kuma ba sa ci. Duk da son da wasu keyin masa amma yakan zaman abin tsoro a wasu lokutan mussamman yayin da ya kamu da ciwon hauka da in ya ciji mutun yakan kaisa barzahu a lokaci kalilan. Ya kan kuma taka muhimmiyar rawa a wajan harkar tsaro ko Isar da sako ga ubangijinsa ta hanyar yin haushi da kuma dabarar da aka koyar dashi.

 

Exit mobile version