Daga Idris Aliyu Daudawa
Farashin shinkafar gida ya fara sauka a wasu manayan kasuwanni a Jalingo jihar Taraba, wani bincike da kamfanin dillanci labarai na ƙasa ya yi, ranar Laraba ya nuna farashin ya sauka, a Gadar Bobboji, Kasuwan Ɓera, da kusuwar mil shida, abin ya nuna lalle farashin ya sauka.
Kamfanin ya jaddada cewar, mudun shinkafa wanda a da ake sayar da shi naira 650 da naira 750, a makonni biyu zuwa uku da suka wuce, yanzu ana sayarwa tsakanin naira450 da kuma550.
Hakanan ma buhun shinkafar gida wanda ake sayarwa tsakanin dubu 28 da dubu 30, a tsakanin mako biyu zuwa uku, yanzu ana sayarwa tsakanin dubu 23 da kuma dubu 24.
Alhaji Nura Mohammed ya ce, dalili da ya kawo faɗuwar farashi ya danganta ne, akan yadda aka kawo ta kasuwa da yawa.
Bugu da ƙari kamar yadda ya ce, ƙyaƙƙyawar daminar da manoma suka samu ita cikin ikon Allah hakan ya bada gudunmawa wajen kawo ta kasuwa da yawa. Ya ƙara da cewar farashin zai iya ƙara faɗuwa ƙasa, wannan kuma ya danganta ne, akan idan aka cigaba da shigowa da ita kasuwa da yawa.
Sai dai kuma kamfanin dillancin labarai na ƙasa ya gano cewar farashin shinkafar waje ya ƙaru, domin kuwa mudu ɗaya da ake sayarwa naira 950 a makonni biyu da suka wuce, yanzu ana sayar da shi naira1,000. Haka kuma buhu mai nauyin kilogiram 50 wanda aka sayar naira dubu18,500 ya tashi saboda yanzu ana sayarwa dubu 19,000 ne.