Farfaɗo Da Kamfanoni Ne Zai Dawo Da Mutuncin Arewa -Marafan Malaman Zazzau

Daga Balarabe Abdullahi, Zariya

An bayyana sai fa an farfaɗo da kamfanoni tare da shugabanci nagari, sannan mutuncin arewa da aka sani shekara da shekaru, zai dawo, ba wasu abubuwa na daban ba.

Marafan malaman Zazzau, Dakta Ɗalhatu Mohammed Jumare,ya bayyana haka a wani taron karrama shi da wata jarida mai zaman kanta ta yi a Zariya a makon da ya gabata.

Marafan Malaman Zazzau, wanda kuma babban malami ne a Jami’ar Ahmadu Bello da keZariya, ya ce farfaɗo da kamfanonin shi zai zai sa matasa da su yi karatu da kuma waɗanda ba su samu damar yin karatun ba, za su sami ayyukan yi, da zai katange su daga aikata wasu muggan ayyuka da ake tsoma su ko kuma suke tsoma kansu.

Ya ci gaba da cewa, duk matsalolin da suke faruwa a jihohin arewa a yau, ba wani abin ke kawo su ba sai rashin ayyukan yi ga matasa, shi ne a ƙarshe suke fara tunanin aiwatar da muggan ayyuka, kamar shiga ƙungiyoyin ta’addanci da garkuwa da mutane da kuma fashi da makami da a shekarun baya ba a san ɗan arewa da yin waɗannan ayyuka ba.

A nan sai marafan malaman Zazzau ya ce waɗanda zasu iya warware waɗannan matsaloli sune gwamnoni, domin farfaɗo da kamfanoni, sai su,domin su ke da kuɗaɗe a hannunsu da ake danƙa musu, domin gudanar da ayyukan da za su ciyar da al’ummarsu gaba.

Ya nunar da cewar, akwai kamfanonin da al’umma suka assasa, a yau sun durƙushe, ko da suna da niyyar farfaɗo da su, ba zai yi wu ba, saboda rashin kuɗi da ake fama da shi a ƙasar,ba wai a arewa kaɗai ba.

Haka kuma Marafan yayi tsokaci na yadda ake yawan furta maganganu marasa tushe ga al’ummar arewa, na ci-ma zaune da dai sauran furucin da ke zubar da mutuncin arewa da kuma ‘yan arewa.

Ya ƙara da cewa, da kafafen watsa labaran da wancan ɓangaren suka mallaka ne ke aibanta al’ummar arewa, tare da faɗin kalaman da suke zubar da mutuncin arewa da kuma ‘yan arewa, amma babu yadda ɗan arewa zai yi ya kare kansa, saboda bai mallaki kafafen watsa labaran ba.

A ƙarshe, Marafan malaman Zazzau ya ce, kowa ya san da arzikin noma da al’ummar arewa suka yi aka gina matatun man fetur, bayan an kashe harkar noma,sai aka koma ɓangaren fetur, shi ne a yau ake cewa arewa ci ma zaune, sun manta su ne ci ma zaune fiye da  shekara  50 da suka gabata.

 

Exit mobile version