A Farfaɗo Da Mutuncin Kaduna -Lamuni

Daga Balarabe Abdullahi, Zariya

An shawarci gwamnan jihar Kaduna Malam Nasir El-Rufa’I da ya haɗa hannu da gwamnonin arewa goma sha tara,su tsara yadda za su dawo da ɗaukakar da garin Kaduna, kamar yadda garin yake a lokacin Sa-Ahmadu Bello da ayarinsa.

Wannan shawara ta fito ne daga wani shugaban al’umma kuma mai tsokaci kan al’amurran yau da kullum mai suna Alhaji Uba Zariya, wanda aka fi sani da Uba Lamuni.

Alhaji Uba Lamuni ya ci gaba da cewar,duk wanda ya san garin Kaduna,kafin turawa su kasance a Nijeriya,ya san garin Kaduna,gari ne da duk wani ɗan Nijeriya ke tinƙaho da garin,musamman a ɓangaren masana’antu da kuma yadda aka samar da cibiyoyin ilimim a garin Kadunan.

Wannan,kamar yadda Alhaji Uba Lamuni y ace shi ya sa hatta wasu jinsi da ba su da alaƙa da jihar arewa sun zo Kaduna tun a wancan shekaru,sun gina kamfanoni sun gina cibiyoyin kasuwanci  sun kuma gina gidajen alfarma da suka ƙara bunƙasa garin Kaduna a shekarun da suka gabata.

A nan ne fitaccen mai tsokaci da al’amurran yau da kullun,y ace da tafiya-ta-yi –tafiya sai matsayin da garin Kaduna ke da shi ya dunga raguwa daga lokaci zuwa lokaci,wannan kuma ya faru ne,a cewarsa,a dalilin rashin kishin wasu magadan Gamji,yadda suka yi sakaci amanar da Sa-Ahmadu Bello ya danƙa ma su a waɗancan shekaru da suka gabata.

Alhaji Lamuni ya bada misali da garin Fatakwal da jinsin inyamurai suka bunƙasa garin da duk abin da za a ce gari ya mallak,da ya shafi kasuwanci da da-dai sauran abubuwa ma su yawan gaske.Ya ci gaba da cewar,kishin jinsin yarbawa ne ya sa garin Ikko ya sami ɗaukaka a ɓangaren kasuwanci da samar da kamfanoni ma su yawa da suke samar da ayyukan yi ga matasan waɗancan yankuna.

Duk ci gaban da aka furta an samu a manyan garuruwa biyu da aka ambata,da arzikin arewa aka bunƙasa su,wato da Auduga da kuma Gyaɗa da al’ummar arewa suka samar da jiɓing goshi,daga baya,in ji shi,sai ake zunɗen ‘yan arewa an ace ma su ci-ma zaune da dai sauran maganganu marasa kyau.

Alhaji Uba Lamuni ya tabbatar da cewar,ya san in har gwamna Malam Nasir El-Rufa’I ya jajirce,kamar yadda ya tashi tsaye a yau wajen ciyar da jihar Kaduna gaba. Kuma,ya ci gaba da cewar,in har gwamna El-Rufa’I ya yi niyyar farfaɗo da garin Kaduna ta haɗa hannu da gwamnonin arewa, abu ne mai sauƙi a wajensa.

A ƙarshen ganawarsa da wakilinmu,Alhaji Uba Zariya,wato Uba Lamuni,yay i kira ga ɗaukacin ma su faɗa-aji a jihar Kaduna su fara tunanin ire-iren gudunmwar da ya dace su bayar ta yadda za a sami damar farfaɗo da mutuncin garin Kaduna a ɗan lokaci kaɗan.

 

Exit mobile version