Connect with us

LABARAI

Farfado Da Masakun Tufafi Arewacin Kasar Nan Zai Magance Talauci

Published

on

An bayyana kokarin da Gwamnan Jihar Kano Dakta Abdullahi Umar Ganduje tare da jajirtaccen matashin dan Kasuwar kantin Kwari Mudassir & Brother’s keyi na kokarin sake farfado da mas’antun da suka durkushe da cewa itace hanya daya tilo da ka iya kawo karshen matsalar talauci da zaman kashe wando da ke zaman barazana ga harkokin tattalin arzikin kasa.

Jawabin Haka ya fito daga bakin guda cikin dattawan Kasuwar Kantin Kwari Alhaji Muhammad Abdullahi Mai Dubji alokacin da yake zantawa da manema labarai a ofishinsa.

Alhaji Mai Dubji yace Babu wata tantama cewa masakun tufafi sune maganin talaucin da ke addabar matasanmu a jihohin arewacin kasarnan, “yanzu Haka dubban ma’aikatun masakun Nijeriya ne tuni suka rasa aikinyi, ya yinda Suma daruruwan manoman auduga suka daina noman audugar sakamakon durkushewar masaku. Har Kuma zuwa Kan ‘yan Kasuwa da su ka daina samun abin sayarwa wanda shi ne sana’ar da suke tun iyaye da kakanni.”

Anyi ittifakin cewa durkushewar wadannan masaku ne musabbabin talaucin da ake fama da shi a arewacin kasarnan bayan Noma da kiwo. Don Haka ya ce akwai bukatar Gwamnatin tarayya tayi duk Mai yiwuwa domin sake farfado da masanantun tufafi a kasarnan

“AlhamdulillahiGwamnan Jihar Kano Dakta Abdullahi Umar Ganduje ya kudiri aniyar Farfado da masakun dake chalawa tare da alkawarin taimakawa duk Masu son kafa masaku a Jihar Kano. Wanda ahalin yanzu ma mashahurin matashin dan Kasuwar tufafi nan dake Kasuwar Kantin Kwari Kuma mamallakin Kamfanonin Mudassir and Brothers ya kudiri aniyar Kafa Masaka Irin ta zamani a Jihar Kano domin samar da ayyukanyi ga dubban jama’a musamman matasa.

Haka zalika Mai Dubji yace Suma masakun dake Kaduna irinsu K.T.L da  U.N.T.L tuni an Fara aikin sake farfado da su, inda ake fatan itama masakar Arewa Tedtile  ta Fara aiki nan bada jimawaba, Haka Suma masakun Zamfara da Funtuwa muna kyautatawa zaton Nan ba da jimawaba zasu Dawo da aiki. Ya kamata mu fahimci cewa dogaro da shigo da tufafi daga kasashen waje Yana da lokaci wanda kuma cike yake da siyasar tattalin arziki tsakanin turawa da Asiya bisa aniyarsu ta mamaye kasashen Africa. Don Haka akwai bukatar Gwamnatin tarayya tayi kokarin dogaro da masakunta musamman na Kano da Kaduna.

A karshe ya ba da shawarar Gwamnati ta bude kofa ga Masu zuba jari domin dawo da ayyukan masakun kasarnan da suka durkushe. Muna kara jinjinawa shugabancin kungiyar Kasuwar Kantin Kwari karkashin jagorancin Alhaji Sharif Sagir Wada bisa kokarin  da suke na ganin an sake farfado da masakun tufafu dake Jihar Kano.
Advertisement

labarai

%d bloggers like this: