Connect with us

DAGA BIRNIN SIN

Farfadowar Kasuwar Sayen Kayayyaki Ta Inganta Tattalin Arzikin Kasar Sin

Published

on

Alkaluman da hukumar kididdigar kasar Sin ta fitar a jiya Alhamis, sun nuna cewa, a farkon rabin shekarar da muke ciki, sana’ar kai sakonni ta farfado cikin sauri bayan kawar da tasirin da yaduwar annobar COVID-19 ke haifarwa, matsakaicin saurin karuwar kasuwanci ya kai 22.5%, adadin da ya kai kusan matsakaicin matsayi na bara.

A matsayinta na kasar dake kan gaba a fannin kasuwancin intanet a duniya, saurin farfadowar sana’ar kai sakonni da kasar Sin ta samu ya nuna alamar farfadowar kasuwar sayen kayayyaki.
Tun daga shekarar bana, yaduwar annobar COVID-19 ta kawo illa ga kasuwar sayen kayayyaki. Wannan ya sa, kasar Sin ta dauki matakai ba tare da bata lokaci ba, don mayar da hadari zuwa matsayin wata dama.
A bisa matakan da ta dauka cikin ‘yan watanni, ya sa yanzu kasuwar sayen kayayyaki na samun farfadowa cikin sauri. A cikin watanni 5 na farkon bana, yawan kayayyakin da aka sayar ta intanet ya karu da kashi 11.5 cikin 100 bisa na makamancin lokacin bara, saurin karuwarsa ya kai kashi 2.9 cikin 100 bisa na watanni hudu na farkon bana. Shugaban kamfanin Nielsen reshen kasar Sin Justin Sargent ya bayyana a kwanan baya cewa, farfadowar kasuwar sayen kayayyaki za ta inganta tattalin arzikin kasar Sin, kana za ta taimaka ga ci gaban tattalin arzikin duniya baki daya.
A cikin ‘yan shekarun da suka wuce, sayen kayayyaki ya kara azama kan bunkasuwar tattalin arzikin kasar ta Sin. Bayan bullar cutar COVID-19, kasashen duniya sun damu kan ko sayen kayayyaki zai iya ci gaba da inganta tattalin arzikin kasar Sin. Yanzu dai, kasar Sin ta kawar da wannan shakku ta hanyar samun farfadowar kasuwar sayen kayayyaki. (Mai fassarawa: Bilkisu Xin)
Advertisement

labarai