Umar A Hunkuyi" />

Farfesa Bagoro Ya Sha Alwashin Saita Alkiblar TETFund

Babban Sakataren gidauniyar tallafawa ilimi ta kasa (TETFund), Farfesa Elias Bogoro, ya yi alkawarin saita al’amurran cibiyar ta yanda za ta zama abin koyi ga saura.

Cikin wata sanarwa da daraktan hulxa da jama’a na hukumar, Mista Benn Ebikwo, ya fitar a Abuja, yana cewa, Bogoro, ya yi wannan alkawarin ne a wajen wani taron ma’aikatan da ke aiki a hukumar a sakamakon naxa shi da Shugaba Buhari ya yi.

“Ina ma Allah godiya a kan yanda aka mayar da ni a bisa mukami na ba tare da na tsammaci hakan ba, wanda hakan bai taba faruwa ba, sai a wannan karon.

“Ban san irin godiyan da zan yi wa Shugaban kasa ba, a bisa lambar yabon da ya ba ni wacce wanidan Nijeriya bai taba samun kaman ta ba, na kuma yi alkawarin yin duk abin da ya dace na saita wannan gidauniya yanda ya dace.

Ba kuma zan taba mantawa da irin tarban da kuka yi mani ba, a lokacin da na dawo bakin aiki na a ranar Litinin, abin har ya ba ni mamaki.

“Ban taba tunanin zan shugabanci cibiyar da muka yi gwagwarmayar ganin tabbatan ta ba tare da kungiyar ASUU.

Ya ce, gidauniyar ita ce fatan farfaxo da kimar manyan makarantu a kasar nan, ta hanyar yanda take tallafa ma su, kamar ta samar ma su da mahimman ayyukan ci gaba, bayar da horo ga malaman jami’o’i da sauran ayyukian ci gaban makarantun.

Ya karfafa cewa, ba wani uzuri ga gidauniyar na ta aiwatar da ayyukan da nagartan su bai cika ba, ya kara da cewa, nagartattun ayyuka ne kaxai gidauniyar za ta rika aiwatarwa.

Babban sakataren ya ce,daya daga cikin manyan manufofinsa shida, shi ne, inganta matsayin ma’aikatan gidauniyar a ilmance, ta hanyar ba su horon da ya dace da inganta matsayin duk wani jami’in da yake a cikinta.

Ya kuma yi alkawarin sake duba wasu al’amurran da suka shafi yanayin aikin hukumar, da kumadaukan matakan da suka dace na inganta al’amurran.

Ma’aikatan sun koka da wasu abubuwa da suka shafi jin daxin su, kamar ababen kula da lafiyar su, da kuma wasu yanayin aiki a harabar cibiyar.

Duk daraktoci, shugabannin sassa da ma’aikatan gidauniyar sun halarci taron.

Exit mobile version