Daga Umar Faruk, Birnin-kebbi
Hukumar zartawa ta jami’ar kimiyya da Fasaha jihar Kebbi da ke Aliero a karkashin shigabancin manjo Janar mai ritaya Muhammad Magoro sun amince da nada Farfesa Bashar Ladan Aliero a matsayin Sabon Shugaban Jami’ar.
Wannan bayyanin ya fito ne a wata sanarwa da Jami’in watsa labarai na Jami’ar, Mallam Husaini Adamu Zuru ya sanya wa hannu.
Jami’in watsa labaran na Jami’ar ya sheda wa LEADERSHIP A Yau cewa sabon shugaban Jami’ar malami ne a Jami’ar Usmanu Danfodiyo, Sakkwato kafin nada shi.
Tuni dai Farfesa Bashar Ladan Aliero karbi madafun iko daga hannu Farfesa Bello Shehu Malami wanda ya kasance shugaban jami’ar har tsawon shekara biyu.