Khalid Idris Doya" />

Farfesa Fanna Abdurahman

Farfesa Fanna Inna Abdurahman ita ce mace ta farko da ta zama Farfesa a cikin matan Kanuri. Mai rikon mukaddashiyar shugabar sashin ilimin kimiyya na Jami’ar Maiduguri. Fanna ta kasance daga cikin bangarori daban-daban na ilimi, kama daga malamar jami’ar har ta zo ta rike mukamin shugabar tsangaya.

 

Wace ce Farfesa Fanna Inna Abdurahman:

An haife ta a Karamar Hukumar Monguno a garin Maiduguri, babban birnin Jihar Borno. Ta fara karatun firamare dinta ne a makarantar Yelwa Central Primaru School da ke Maiduguri, ta kuma halarci kwalejin tarayya da ke Owerri a Jihar Imo inda ta fita da takardar shaidar kammala sakandari a wannan kwalejin a shekara ta 1980.

Har-ila-yau, ta samu shaidar digirinta na farko ‘Bsc’ a sashin ilimin sinadarai ‘Chemistry’ a jami’ar Maiduguri a shekara ta 1987, ba ta yi kasa a guiwa ba, ta kuma sake nausa don neman ilimi matakin mastarin digiri dinta a fannin ilimi mai zurfi kan sinadarai a 1992. Ta ci gaba da zafafa neman ilimi, wadda ta taka matakai daban-daban har ta yi nasarar zama Farfesa a shekara ta 2011.

Farfesa Fanna Inna ta wallafa littafai da kuma kasidodi sama da 120 a matakai tun daga na yanki har zuwa matakin kasa ta kuma nausa da wallafe-wallafenta zuwa matakin kasa da kasa wadda kuma ta sha halartar manyan taron kara wa juna sani a fadin duniyar nan wacce ta fi yawaita gabatar da faifofinta a kan sinadarai da yanayin muhallai.

Farfesa Fanna ta taka matakai daban-daban a fannin ilimi kama daga bangaren koyarwa da kuma bangaren gudanarwa ‘iyayen mulki’ na jami’a, daga cikin sun hada da shugabar sashin tsangayar ilimin sinadarai, ta kuma shugabanci sashin bincike na ‘Lembir Board of Research’ shugabantar cibiyar harkokin kimiyya ta jami’ar Nijeriya da dai sauransu.

Mace ce wacce ta tashi tsaye wajen yin aikin ba tare da gajiyawa ba, wannan dalilin ne ma ya bata dama ta ci gaba da tsunduma fage rayuwa daban-daban domin nuna wa duniya cewar mata ma suna da muhimmanci wajen ci gaban kasa.

Ta Ina Ne Farfesa Fanna ta yi zarra wa sa’a?

Farfesa Fanna ita ce mata a cikin Kanuri ta farko da ta zama shugaban tsangayar ilimi a jami’a, ita ce Farfesa ta farko a dukkanin matan Kanuri, ita ce mace ta farko da ta zama mai rikon mukamin shugaban sashi guda ‘DEAN’ a jami’a, har-ila-yau ita ce mace daya tilau ta farko da za ta iya zama Dean na tsangaya guda.

Farfesa Fanna, ta kasance shugaban tsangaya HOD a tsangayar ilimin sinadarai sama da shekaru takwas, har ta zo ta zama mai rikon shugaban sashin ilimin kimiyya gaba daya na jami’ar, ba ga wannan ta kuma rike mukamai masu tarin yawa har zuwa gay au tun lokacin da ta fara aiki a wannan jami’ar.

Fanna tana daga cikin mambobin kwamitin saita jami’ar Jihar Borno, yanzu haka Fanna Daraktace a cibiyar nan ta ‘Center for Research and Innobation’ na jami’ar.

A bisa jajircewarta ne, ‘yan uwa da abokan arziki suka shirya mata wani gawurtaccen taron murna da kuma yin gawurtaccen bikin murna da samun zamanta ‘Farfesa’ wadda suka shirya a ranar 5/6/2015 wadda aka yi a dakin taro na Elkanemi a birnin Maiduguri.

Taron ne wadda ya daukaka lifafarta, aka tara taron jama’a masu fada a ji wadda hakan ma ya sake fito da Fanna duniya ta sanya wacce hakan ya sanya ta samu kanta daga cikin fitattun mata a wannan lokaci.

Fanna ta bayyana cewar kasancewarta mace hakan bai nuni da cewar ba za ta iya taza wani abu na rayuwa ba, hakan ne ya bata dama ta tsunduma gogayya da dukkanin wani irin mutum domin ta samu cimma burinta. Fanna Inna ta shawarci mata da cewar su tashi tsaye wajen neman ilimi domin yanzu an zo wani lokacin da ilimin ked a matukar muhimmanci ga rayuwar bil adama musamman ga su mata, har-ila-yau, Fanna ta bayyana cewar jajircewarta da kuma tsayuwar dakar da yi shi ne ya kawo ta ga samun matsayi na Farfesa, wadda kuma ta bayar da gudunmawa sosai ta fuskacin ci gaban ilimi da kuma inganta koyo da koyarwa musamman a Jami’ar Maiduguri.

 

Exit mobile version