Connect with us

DAGA BIRNIN SIN

Farfesa Jami’ar Oxford: Akwai Tantama Game Da Asalin Cutar Covid-19

Published

on

Kwararren malami dake koyarwa a jami’ar Oxford Dr Tom Jefferson, ya ce mai yiwuwa kwayoyin cutar COVID-19, sun jima kwance a sassa daban daban na duniya, kafin su samu kyakkyawan yanayin kyankyashewa, sabanin zaton da wasu ke yi cewa kasar Sin ce asalin cutar.

Dr Tom Jefferson, ya ce akwai wasu shaidu dake nuni da cewa, kwayoyin cutar sun kasance a wasu yankuna na duniya kafin bullar su a nahiyar Asiya.

Ko da a makon jiya ma, wani kwararren masanin kwayoyin cututtuka na kasar Sifaniya, ya bayyana gano birbishin kwayoyin cutar, a wasu samfuran ruwa da aka gwada cikin watan Maris na shekarar bara, kimanin watanni 9 kafin bayyanar cutar a kasar Sin.

Kaza lika wasu masana kimiyya na kasar Italiya, sun gano kwayoyin cutar cikin wani ruwan dagwalo a biranen Milan da Turin, tun a tsakiyar watan Disamba, makwanni da dama kafin gano masu dauke da cutar a karon farko. Har ila yau, wasu kwararrun sun gano birbishin kwayoyin cutar a kasar Brazil tun cikin watan Nuwambar bara.

Cikin wani bayani da aka wallafa a jaridar Telegraph, Dr Jefferson tare da daraktan cibiyar bincike ta CEBM farfesa Carl Henegehan, sun yi kira da a zurfafa bincike game da cutar ta COVID-19.

Dr Jefferson ya ce, tuni suka fara fadada nazari, tare da duba yanayi na muhalli, da muhallin rayuwar nau’oin wannan kwayar cuta, wadda kawo yanzu ba a da cikakkiyar masaniya game da ita.  (Saminu Hassan)
Advertisement

labarai